Header Ads

Sojojin Sudan sun zargi dakarun RSF da kashe gwamnan Darfur ta Yamma

Shugaban sojojin kasar Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan da shugaban RSF, Mohamed Hamdan Dagalo

Sojojin Sudan a ranar Laraba sun zargi dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF) da "sacewa da kuma kashe" gwamnan jihar Darfur ta Yamma, Khamis Abdullah Abakar, yayin da yanzu ake kusan wata biyu na kokarin neman iko tsakanin janarorin guda biyu wanda hakan ya jefa kasar cikin mummunan yaki.

Kashe Khamis Abdullah Abakar na nufin RSF sun kara wani "Babi a cikin munanan laifukansu da suke aikatawa a kan baki daya mutanen Sudan." Kamar yadda sojojin suka bayyana a kafar sada zumunta ta Facebook, inda ta kira al'amarin da "mummunan aiki."

No comments

Powered by Blogger.