Header Ads

Sojojin Isra'ila sun yi harbi kan 'yan jaridu a Jenin

Bafalasdine dan jarida mai daukar hoto, Hazem Nasser

Sojojin Isra'ila a ranar Litinin sun harbi wani dan jarida mai daukar hoto wanda ke daukar yadda ta ke cigaba da ayyukan zalunci a birin Jenin da ke arewacin yamma da Gabar kogin Jordan.

Kamar yadda Quds News Network ta bayyana, an harbi Hazem Nasser ne lokacin da sojojin mamayar suka yi wani kutse a birnin da ke nuna turjiya a ranar Litinin.

An bayyana halin da ya ke ciki da tsaka-tsaki da kuma wanda ya ta'azzara, inda a yanzu ake yi masa tiyata.

Wannan na zuwa ne bayan arangama mai karfi da ta barke a tsakanin mayakan fafutika da sojojin gwamnatin Isra'ila bayan da Isra'ilan ta yi kutse a Jenin.

A yayin arangamar, sojojin Isra'ila sun kashe akalla Falasdinawa hudu tare da raunata gomomin wasu ta hanyar harbi da harsasai masu rai.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito, kwararrun masu harbi na mai mamaya Isra'ila an bayyana sun yi harbi kai tsaye kan 'yan jaridu wadanda ke daukar irin zaluncin gwamnatin a Jenin, 'yan mitoci kadan daga wurin da aka kashe kwararriyar 'yar jarida Shireen Abu Akleh a shekarar da ta gabata.

A farkon wannan watan, sojojin Isra'ila suna sane suka harbi wani dan jarida mai daukar hoto mai suna Momen Samreen a kai yayin da ya ke daukar rushe gidajen da Falasdinawa suka mallaka a birnin Ramallah da ke yamma da Gabar kogin Jordan.

No comments

Powered by Blogger.