Header Ads

Sojojin Isra'ila sun kashe wani Bafalasdine mai shekaru 20 a Nablus

Shahid Khalil Al-Anis

Sojojin Isra'ila sun kashe wani bafalasdine mai shekaru 20, Khalil Al-Anis, ta harbinsa a kai yayin wani kutsen soji da suka yi a barnin Nablus a ranar Alhamis.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Arab News ta ruwaito, arangama ta barke ne bayan da sojojin na Isra'ila suka rushe gidan wani da ke tsare mai suna Osama Al-Taweel.

Hukumar Palestinian Red Cross ta bayyana cewa wasu mutanen kusan 337 - ciki harda yara hudu - suka raunata sakamakon harsasai da gas, biyu daga cikinsu wanda ya ta'azzara, a yayin arangamar.

Bayan haka, sojojin Isra'ila kai tsaye sun harbi motar asibiti ta Falasdinawa da harsasai masu rai da gurneti, wanda suka lalata gilashin gaban motar. Wadanda ke yin taimako domin kula da lafiya da ke ciki basu samu rauni ba.

Bayan kashe Al-Anis, kawo yanzu Falasdinawa da sojojin Isra'ila suka kashe ko kuma yahudawa yan-kama-wuri-zauna ya karu zuwa 167. Kididdigar ta hada da mutane 36 daga zirin Gaza wadanda aka kashe a watan Mayu da ya gabata.

Firaministan Falasdinawa, Mohammed Shtayyeh, ya zargi Isra'ila da sake mamaye yamma da gabar kogin Jordan da kuma keta dokokin kasa-da-kasa da kuma dokar ayyukan jin kai.

Ya bayyana cewa yankunan Falasdinawa na fuskantar kutse daga sojojin Isra'ila, wanda ya hada da zuwa masallacin Al-Aqsa; hari wanda ake harbi domin a kashe; kama mutane; da kuma kwace filin kasa domin fadada yin gine-gine.

Nabil Abu Rudeineh, kakaki na musamman ga shugaban kasar Falasdinawa, ya bayyana cewa cigaba da dagula al'amurra da Isra'ila ke yi zai iya jefa yankin cikin tashin hankali da rudani. 

Ya yi Allah wadai da afkawa Nablus din da aka yi a ranar Alhamis, kashe Al-Anis da kuma tarwatsa gidan Al-Taweel, inda ya kara da cewa siyasar yin horo ga mutane baki dayansu da Isra'ila ke yi - ko ta hanyar rushe gidaje, kashe 'yan kasa ko kuma zagaye Jenin da Nablus - laifin yaki ne a karkashin dokar kasa-da-kasa.

Dole ne a hukunta Isra'ila domin wadannan laifuffuka tare da daukar kwararan matakai domin hana ta aikata wasu, kamar yadda ya bayyana.

Janar Akram Rajoub, gwamnan Jenin, ya bayyana cewa niyyar 'yan Isra'ila shine su wanzar da iko a baki daya yamma da gabar kogin Jordan, daga mutanenta zuwa kasarta zuwa albarkatunkatun ta.

Ya bayyanawa Arab News cewa kutsen da sojojin Isra'ila ke yi kusan kullum a Jenin babu dalilin yinsa, domin babu wata barazanar tsaro ga 'yan kasar Isra'ila da ke wurin.

No comments

Powered by Blogger.