Header Ads

Sama da yara miliyan 449 a faɗin duniya ke rayuwa a yankunan da ke fama da rikici - Ƙungiyar Save the Children

Wasu yara a yankin da ke fama da rikici

Sama da yara miliyan 449 ke rayuwa a yankunan da ke fama da rikici a shekarar 2021, kamar yadda kungiyar kasa-da-kasa mai zaman kan ta mai suna Save the Children ta ruwaito.

A shekarar 1982, majalisar dinkin duniya ta ayyana ranar 4 ga watan Yuni a matsayin ranar yara wadanda basu da laifi masu fuskantar tursasawa ta kasa-da-kasa, wadda aka sadaukar ga yara Falasdinawa da 'yan kasar Lebanon wadanda hare-haren Isra'ila ya shafa.

Kusan keta ka'idoji 24,000 aka ruwaito a kan yara a lokutan da ake yake-yake a shekarar 2021 kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na majalisar dinkin duniya.

Laifuffukan da aka fi aikatawa ga yara sune kisa, haifar da matsala ga wani bangaren jikinsu, daukar su domin shiga yaki, da kuma hana su kaiwa ga kayan agaji.

A cikin rahoton na Teghrib News Agency, yara 2,515 aka kashe yayin da kuma yara 5,555 suka zama masu nakasa a daidai lokacin, kamar yadda rahoton ya ruwaito.

A cikin shekarar 2021, Afghanistan, Jamhuriyar Damakaradiyyar Congo, Isra'ila, Falasdinu, Somaliya, Siriya da Yemen na cikin kasashen da aka fi aikata laifuffuka a kan yara.

A yayin da laifin sace yara ya karu zuwa kashi 20 cikin 100, laifin da ya shafi mutuntakar su ya karu sama da kashi 20 cikin 100 daga shekarar da ta gabata.

No comments

Powered by Blogger.