Header Ads

Ruwan sama da iska mai ƙarfi sun yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutane 27 a Pakistan

Wani mutum daga hagu da kuma wani matashi yayin da suke amfani da faifan dish wajen kwasar yara daga wani yanki da aka yi ambaliyar ruwa saboda ruwa mai ƙarfi a yankin Jaffarabad, Baluchistan a ranar 26 ga watan Agustar 2022.

Ruwan sama mai karfi wanda iska mai karfi ta biyo bayansa ya yi sanadiyyar rasuwar akalla mutane 27, ciki har da yara takwas a arewa-maso-yammacin kasar Pakistan kamar yadda jami'ai suka bayyana a ranar Lahadi.

"Akalla mutane 12 rufi da katangun gidajensu da suka rushe suka rufe su da ransu." Cewar Taimur Ali Khan, kakakin hukumar kula da annoba ta yankin ya shaidawa AFP. 

Ruwan da iskar sun samu yankuna hudu ne na Khyber Pahktunkhwa, inda mutane 15 suka rasu a yankin Bunu, ciki har da wasu da suke 'yan uwa ne da shekarunsu ke tsakanin biyu zuwa 11.

Sama da mutane 140 ne suka raunata inda kuma sama da dabbobi 200 ne suka mutu.

Hukumomi sun ayyana dokar ta baci a duka yankunan guda hudu.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Arab News ta ruwaito, a cikin shekarar da ta gabata, Pakistan ta fuskanci ruwa da ba a taba yin kamar sa ba inda ya sa ambaliya a kashi uku na kasar, sanadiyyar haka kuwa ya lalata gidaje miliyan biyu tare da rasa rayukan mutane 1,700.

A yanzu haka, a kudancin kasar , hukumomi sun ce guguwa na nan za ta karaso Pakistan da Indiya daga tekun Arabiya.

A cikin wani jawabi daga hukumar kula da annoba ta yankin Sindh, ta yi gargadin samun ruwa da iska mai karfi da za su iya kaiwa kilomita 100 cikin awa daya daga baya a cikin satin nan.

"Ana ba masu kamun kifi shawarar kada su shiga can cikin tekun har sai abubuwa sun dawo daidai zuwa ranar 17 ga watan Yuni." Kamar yadda ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.