Header Ads

Palasdinawa 586 aka kashe a cikin shekaru 4 da rabi saboda rashin daukar mataki daga 'yan sanda a Isra'ila

Dubunnan mutane na gudanar da zanga-zanga sakamakon kisan mutane biyu da 'yan sanda suka yi a arewacin birnin Tamra da ke Isra'ila a ranar 2 ga watan Fabrairun shekarar 2021.

Falasdinawa 'yan kasar Isra'ila 586 aka kashe daga watan Janairun shekarar 2018 zuwa yau, sakamakon hauhawar laifuffuka da rashin daukar mataki na 'yan sanda.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta ruwaito, bayanin 'yan sandan Isra'ila na tsakanin shekarun 2018 zuwa 2022 ya nuna cewa akwai kisan kai 690 da aka yi a cikin shekaru hudu (ciki har da Jerusalem da yankin da aka mamaye na Golan Heights) kuma an kashe mutane 731, inda kashi 70 cikin 100 daga al'ummar Larabawa suka fito, kamar yadda shafin Walla na Isra'ila ya bayyana.

Bayanin ya nuna cewa yawan larabawa da abin ya shafa ya kusa lunkawa sau uku a kan na al'ummar Yahudawa a daidai lokacin. 

Wasu mutane 77, ciki da mata shida da yara biyu an kashe su tun bayan shigowar shekarar nan. Wannan bai hada da wadanda kisa ya shafa a Jerusalem da yankin da aka mamaye na Golan Heights ba, wanda ya kai yawan wadanda suka mutu zuwa 587 a cikin shekaru hudu da rabi.

Bayanin ya bayyana cewa a garuruwan Larabawa ne aka fi fuskantar rikice-rikicen da kisan kan a tsakanin shekarun 2018 zuwa 2022, garuruwan sune Jirs Al-Zarqa, Tuba Zangariyya, Kafr Yasif, Al-Tira da Turan a yayin da kuma Tel Aviv, Jaffa, Acre da Nof Hagalil suna cikin garuruwan da suke a yamutse wadanda aka fi samun rikice-rikice da aiwatar da kisan kai kamar yadda Walla ta bayyana.

Shafin ya ma ruwaito cewa kashi 95 cikin 100 na kisan kai ana yin su ne da bindiga, kuma 'yan sandan Isra'ila sun nuna cewa yawan Larabawa da suka rasa rayukansu ya zuwa 3 ga watan Mayu na shekarar 2023, na da yawa matuka fiye da yawan wadanda suka rasa rayukansu a cikin shekaru biyu da suka gabata a gwargwado a cikin watanni. 

Bayanin ya ma nuna cewa yawan Larabawa da suka rasa rayukansu tun farkon wannan shekarar ya lunka fiye da sau biyu in an kwatanta da daidai wannan lokacin a shekarar da ta gabata ta 2022.

No comments

Powered by Blogger.