Header Ads

Me ya sa 'yan sanda suka kewaye harabar majalisar dokokin jihar Nasarawa?

Majalisar dokokin jihar Nassarawa

Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa sun kewaye harabar majalisar jihar Nasarawa domin hana karya doka da oda.

Wannan na zuwa ne bayan an samu kakakin majalisa a jihar mutum biyu a majalisar jihar ta bakwai.

Jami'in dan sanda mai kula da hulda da jama'a na jihar (PPRO) DSP Ramhan Hansel ne ya bayyana haka a ranar Laraba a cikin wani jawabi a Lafiya.

Nansel ya ce daukar matakin ya zo ne biyo bayan umarni daga kwamishinan 'yan sandan jihar, Mr Maiyaki Mohammed-Baba. 

Ya bayyana cewa kwamishinan ya bada umarnin bayan tattaunawa da sauran hukumomin tsaro da ke jihar.

Zababbun mambobin majalisar a ranar Talata, 6 ga watan Yuni sun yi zama daban-daban guda biyo wanda ya haifar da zaben kakakin majalisa guda biyu ga majalisar. 

An dai ga jami'an tsaro masu yawan da ba a saba gani ba a harabar a ranar Laraba kamar yadda kamfanin dillancin labarun Nijeriya (NAN) ya ruwaito.

No comments

Powered by Blogger.