Header Ads

Me ya sa tattaunawa a tsakanin tawagar Afirka da Putin ke da muhimmanci?

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, na tattaunawa da tawagar shugabannin Afirka a Fadar Constantine.

Tawagar wakilin Afirka sun tattauna da shugaban kasar Rasha a wani yunkuri na kawo karshen rikicin Ukraine, wani abu da ke yin nuni da yadda wani al'amari a duniya na yaki a Ukraine ke iya shafar Afirka.

Cewa Afirka na kokarin kawo karshen yaki a gabashin turai abu ne babba.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya karbi bakuncin wata babbar tawagar shugabannin Afirka a St Petersburg domin tattauna yadda za a kawo karshen rikicin Ukraine.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Tehran Times ta ruwaito, a yayin tattaunawar Putin ya yi maraba da irin "daidaitacciyar matsaya" ta tawagar dangane da rikicin tare da bayyana cewa Rasha ba ta taba kin tattaunawa domin samar da zaman lafiya ba.

Tawagar ta kasar Afirka ta hada da shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, shugaban kasar Sanagal, Macky Sall, shugaban kasar Komoros, Othman Ghazali, shugaban kasar Zambiya, Hakainde Hachilema, Firaministan Misra, Mostafa Madbouly da manyan jami'ai daga Jamhuriyar Kongo da Uganda.

Wannan na da muhimmanci kuma yana nuni da hatsarin da rikicin ke da shi ga nahiyar Afirka, kamar yadda kafar ta ruwaito.

Tuni dama kasar Sin ta yi kokarin kawo karshen yakin, Iran ita ma ta yi haka, shugaban kasar Brazil, Lula da Silva, shima ya yi kokarin hakan a 'yan kwanakin baya, kamar yadda saura da yawa suka yi, in ban da kungiyar NATO da Amurka ke jagoranta da kawayensu (ban da kasar Turkiyya).

Yakin ya shafi tattalin arziki a fadin duniya, amma Afirka ta fi shan wahalhalunsa inda ta fi fama da sakamakon rikicin.

Kafin yakin ya barke, Afirka ta dogara sosai a bangaren makamashi da abinci daga duka Rasha da Ukraine.

Bayan barkewar yakin a cikin watan Fabrairun shekarar 2021, shigo da hatsi, wanda ke da matukar muhimmanci musamman ga Afirka an tsayar da shi.

An cigaba da fitar da shi ta tekun Black Sea a karkashin wata yarjejeniya ta majalisar dinkin duniya da aka kara tsawaitawa zuwa watan Mayu na wannan shekarar zuwa wasu watannin biyu har sai ranar 17 ga watan Yuli.

Sai dai kasashen Afirka suna korafin cewa mafi yawan hatsin, a karkashin yarjejeniyar ta majalisar dinkin duniya, ana tafiya da shi kasashen turai ne da cewa Afirka, inda nan ne aka fi bukatarsa, ba ta samun kason ta da ya dace.

Putin ya bayyana hakan a cikin jawabin da ya yiwa tawagar ta Afirka.

"Ya zuwa 15 ga watan Yuni, tan miliyan 31.7 na albarkatun noma aka fitar daga tashar jirgin ruwa ta Ukraine, yayin da tan 976 ko kashi 3.1 a cikin 100 aka kai kasashen Afirka wadanda su suka fi bukata." Kamar yadda Putin ya bayyana.

A sakamakon haka, abinci ya kara tsada inda dama tuni mutane da dama suna cikin talauci. 

A yayin tattaunawar da Putin, shugabannin na Afirka sun bayyana cewa yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine ya yi mummunan shafar baki daya nahiyar Afirka, inda ya haifar da barazana ga abinci da makamashi da ba a taba gani ba. 

Tun kafin nan, tawagar ta Afirka ta ziyarci kasar Ukraine dauke da irin shirin na neman zaman lafiya ga duka shugabannin kasahen biyu, a yunkurinsu na kawo karshen rikicin, wanda ba ya nuna alamun kawo karshe.

Kiran da Afirka din ta yi na zaman lafiya ya nemi a dage duka wata dakatarwa da aka yi wa safarar hatsi da sauran kayayyaki nan take, wadanda kuma yakin ya shafa a samar masu kayan jin kai. 

Fatar tawagar ta Afirka na kawo karshen yakin a dukkan alamu ba ta kai ga nasara ba, kamar yadda ya kasance da saura wadanda suka yi yunkurin kawo karshen yakin.

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ki amincewa da duk wata tattaunawar zaman lafiya da Rasha, duk da neman tawagar na ya janye da kuma cewarsu wannan yakin ba zai cigaba har abada ba.

Duk da haka, Afirka na nuna abinda mafi yawan kasashen duniya ne suka yi: daidaitacciyar matsayarta game da yakin.

Duk da cewa ta san rawar da NATO ke takawa wajen tsawaita yakin ta hanyar aikawa da makamai da kudinsu ya kai dalar Amurka biliyan 100 da sauran taimako, Afirka na nuni da cewa ba ta goyon bayan wani bangare, ta na so ne kawai yakin ya zo karshe.

Putin ya shaidawa tawagar cewa a farkon kwanakin yakin, lokacin da aka yi tattaunawa kai tsaye a tsakanin Rasha da Ukraine a Istanbul, Moscow na da shirin yarjejeniya da Kiev domin kawo karshen yakin.

Ya nunawa tawagar wani kundi inda ya ke fadin, "Shi ne wannan. Akwai shi. Shi ne ake kira da - yarjejeniya ta kasancewar Ukraine 'yar ba ruwana tare da tabbatar da tsaron ta. Ya shafi tabbaci ne." 

Shugaban na Rasha ya ma bayyana cewa matsalolin abinci da makamashi da ke cigaba ba sun faru ba ne sakamakon abinda Rasha ke kira da "aikin soji na musamman" a Ukraine, amma sakamako ne na matakan kasashen yamma.

A yayin da bangarorin duniya ke cigaba da kokari wajen kawo karshen yakin da ke shafar bangare mai girma na duniya, yana kara fitowa fili a kullum cewa kungiyar NATO karkashin jagorancin Amurka ba bukatarta zaman lafiya ga mutanen Ukraine, Rasha, Afirka ko kuma daidaituwar tattalin arzikin duniya ba, kamar yadda ya ke a cikin rahoton.

No comments

Powered by Blogger.