Header Ads

Ka mai da ba da bashi ga dalibai zuwa ba da tallafi ga dalibai marasa ƙarfi - Ƙungiyar ASUU ga Tinubu

Wasu ɗaliban jami'a cikin zauren daukar karatu

Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) ta nemi shugaban kasar Nijeriya, Bola Tinubu, da ya mayar da sabon kudirin ba dalubai bashi zuwa bayar da tallafi ga dalubai 'yan kasa.

"Wannan zai fi idan muna bayarwa ne ga daluban da suke ba su da karfi, ya kamata ne a kira shi tallafi ba bashi ba." Kamar yadda shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana a cikin shirin _Sunday Politics_ na tashar talabijin din Channels Television.

"Ya kamata ne a kira shi da tallafi tunda yana fitowa ne daga ma'ajiyar gwamnatin tarayya (Federation Account) ba wai za su samu bane bayan sun kammala karatu, suna da nauyi sosai kuma a cikin shekara biyu, in ba su biya ba, za su tafi kurkuku. Shi ya sa mu ke magana a kan tattaunawa daga kowanne bangare, ka samu ra'ayoyi daga ko'ina." 

A dai ranar Litinin ne Tinubu ya sanya hannu a kudirin dokar bayar da bashi ga dalubai domin cika alkawarin da ya yi yayin gudanar da kamfe. Kakakin majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, ne ya dauki nauyin sa, wanda a yanzu haka shine shugaban ma'aikatan shugaban kasa. Yanzu a matsayinsa na doka, dokar ta tanadar da bayar da bashin da ba ruwa a cikinsa ga dalubai marasa karfi 'yan Nijeriya.

Sai dai, shugaban na ASUU ya bayyana cewa ba za a iya gabatar da bayar da bashin ba. Ya bayyana cewa, "Ba za a iya cigaba da yin sa ba." 

Kamar yadda Osodeke ya bayyana, "Tunanin bayar da bashi ga dalubai ya zo ne a shekarar 1972 kuma a banki ne wanda aka tanadar. Mutanen da suka karbi bashin ba su biya ba, za ku iya zuwa ku bincika. A shekarar 1994, 1993, gwamnatin soji ta samar da Decree (doka) ta 50 inda ta kafa hukumar bayar da bashi ga dalubai. A shekarar 2014, majalisar kasa ta mayar da shi wani al'amari na gida, a cikin shekara daya ya zo karshe. Kudaden suka bace. Muna so mu ga yadda wannan zai banbanta." 

Kamar yadda shugaban na ASUU ya bayyana, akwai sama da dalubai miliyan daya a jami'o'i mallakin Nijeriya, kuma bashin ba zai iya biyan kudin makarantar su ba.

Shugaban na ASUU ya bayyana cewa ka'idojin bashin "ba za a iya bin su ba." Inda ya kara da cewa sama da kashi 90 cikin 100 na daluban ba za su iya iya bin "tsauraran matakan" samu da biyan bashin ba.

"Mu a matsayinmu na kungiya, mun yi bincike kasashen da ke fadin duniya, na mutanen da suka amfana da wannan bashin, suna kashe kawunansu. A cikin 'yan kwanankin nan, (shugaban kasa Joe) Biden ke kokari domin ya mayarwa bankuna wasu daga cikin basussukan da aka karba a Amurka." Kamar yadda ya bayyana.


"Zai fi in an samu wata hanyar samar da kudade ga ilimi ba dora nauyin bashi ga daluban da iyayensu ke daukar naira 30,000 a wata ba."

No comments

Powered by Blogger.