Header Ads

Isra'ila na shirin "raba" harabar masallacin al-Aqsa a tsakanin Musulmi da Yahudawa


Kamar yadda kafar watsa labaru ta Press TV ta ruwaito, kafofin watsa labarun Falasdinawa sun yi gargadi dangane da shirin gwamnatin Isra'ila na "raba" lokaci da wuri a harabar masallacin al-Aqsa da ke tsohon birnin al-Quds da aka mamaye a tsakanin Musulmai da Yahudawa a yayin da Tel Aviv ke kara kaimi wajen fadada mamayar ta da zaluncin zalunci.

Wani mamban Knesset din gwamnatin, Amit Halevi, da ke jam'iyyar Likud Party da ke da tsatstsauran ra'ayi ne ya kirkiro shirin da ke da niyyar raba masallacin mai tsarki a tsakanin dumbin musulmai da ke zaune a al-Quds da kuma yahudawa yan-kama-wuri-zauna da ke da tsatstsauran ra'ayi da ke ikirarin suna da 'yancin su yi "addu'a" a harabar, kamar yadda jaridar larabci ta Al-Ayyam daily newspaper ta ruwaito a ranar Alhamis.

Jaridar ta kara da bayyana cewa Halevi ya yi kira da a ware kudancin harabar ga Musulmai, yayin da kuma tsakiya da bangarorin arewaci da ya hada da Qubbat as-Sakhra (the Dome of the Rock) ga Yahudawa masu tsatstsauran ra'ayi. 

Dan siyasan na Isra'ila cikin alfahari ya ma bayyana cewa shirin sa na da niyyar kawar da kulawar da gwamnatin kasar Jordan ke yi ne ga masallacin al-Aqsa.

Jaridar da ke fitowa kullum da ke Ramallah, Al-Hayat al-Jadida, ita ma ta ruwaito Ma'aikatar Falasdinawa ta Harkokin al-Quds na yin watsi da wannan shirin a matsayin wani shiri da ke yunkurin tonon fada matuka, inda ta yi ikirarin zai kara ruruta zaman dar-dar ne da ake ciki wanda zai hadu ya haifar da rikici mai girma.

Bayan haka, Sheikh Muhammad Ahmad Hussein, wanda shine babban malami a al-Quds, shima ya jiwo yunkurin hukumomin Isra'ila na Yahudantarwa da raba masallacin al-Aqsa, kyale yahudawa yan-kama-wuri-zauna yin addu'a a wurin da ya fi ko'ina muhimmanci tare da canza tarihinsa da matsayarsa a doka.

Sai ya bayyana cewa wannan shirin na hukumomin Tel Aviv zai tayar da rikicin da zai iya shafar duniya baki daya. Sheikh Hussein ya ma dora alhakin abubuwan da za su biyo baya ga hukumomin kasar kan cigaba da tunzura zaman dar-dar a gabar yamma da kogin Jordan da aka mamaye.

Ya ma bayyana yunkurin gwamnatin Tel Aviv na kirkiro tarihi wanda ya ta'azzara a 'yan kwanakin nan, inda ya bayyana cewa tarihin masallacin al-Aqsa mai albarka kowa ya san shi, kuma majalisun duniya sun tabbatar da cewa mallakin Musulmai ne tare da watsi da shu'umin shirin gwamnatin na raba lokaci da wuri a harabar.

Babban malamin na al-Quds sai ya yi kira ga kasashen duniya da su yi aikin da ya rataya kansu, su shigo nan-da-nan su iyakance hukumomin Isra'ila, su hana su aiwatar da shirin su a kan masallaci mai tsarki na al-Aqsa, su kuma samar da matakai da za su hana barazana ga wurare masu tsarki na Falasdinawa.

Harabar masallacin al-Aqsa na kusa da Western Wall plaza ne, wanda ya hada da Qubbat as-Sakhra (the Dome of the Rock) da kuma masallacin al-Aqsa.

Kamar yadda ya ke a cikin yarjejeniyar da aka sa wa hannu a tsakanin gwamnatin Isra'ila mai mamaya da gwamnatin kasar Jordan bayan Isra'ila ta kama gabashin al-Quds ba bisa ka'ida ba a shekarar 1967, an haramta yin ibadar da ba ta musulmai ba a masallacin al-Aqsa.

Mafi yawan mambobin majalisar Isra'ila ta Knesset masu tsatstsauran ra'ayi ne wadanda ke goyon bayan a rushe wuraren musulunci masu tsarki a gina haikali na Yahudawa a maimako. 

Falasdinawa na neman iko da gabar yamma da kogin Jordan da aka mamaye a matsayin wani bangare na kasar su mai 'yancin kan ta tare da kallon yankin gabashin al-Quds a matsayin babban birnin su a nan gaba.

No comments

Powered by Blogger.