Header Ads

Iran, Saudi Arabiya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman za su gabatar da atisayen sojojin ruwa na haɗaka

Wani jirgin sojojin ruwa mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Kasar Iran, Saudi Arabiya, Hadaddiyar Daular Larabawa da Oman za su gabatar da atisayen sojojin ruwa na hadaka, kamar yadda wani shafin yanar gizo na kasar Katar ya ruwaito.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta bayyana, Al-Jadid ce ta yi rahoton a ranar Juma'a inda ta bayyana cewa kasar Sin tuni ta shiga tsakani wajen sasantawa a tsakanin Tehran, Riyadh da Abu Dhabi da niyyar tabbatar da tsaron tafiye-tafiyen cikin ruwa a yankin ruwan da ke da matukar muhimmanci.

A baya a cikin watan Maci, Beijing ta yi nasarar tattaunawa da sasantawa a tsakanin Tehran da Riyadh wanda ya sa manyan kasashen biyu da ke yankin tekun Fasha sa hannu a cikin yarjejeniyar da ta dawo da dangantakar diflomasiyyar su.

Kamar yadda masu sa ido kan yadda al'amurra suka bayyana, yardar da kasashen yankin tekun Fasha din suka yi da shiga tsakanin kasar Sin na yin nuni da yadda ikon kasar ke kara yawa a yankin ba kamar yadda ikon Washington ya ke ba.

Tun bayan nasarar yin juyin-juya halin musuluncin a Iran a shekarar 1979, Jamhuriyar Musuluncin ba ta goyon bayan shisshigin kasashen waje a yankin, inda ta ke cewa al'amurran da suka shafi yankin wadanda suke yankin ne ya kamata su kula da su da kansu.

Na baya-bayan nan kuwa shine wanda ya faru a ranar Juma'ar da ta gabata, inda shugaban jami'an kariya ga juyin-juya hali na musulunci (IRGC) na sojojin ruwa kai tsaye ya yi watsi da kasancewar sojojin Amurka a tekun Fasha da sunan samar da tsaro ga ruwan yankin.

Ita kuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, ta bayyana cewa za ta dakatar da sojojin ruwa wadanda Amurka ke yiwa jagoranci.

A ranar Laraba, shafin yanar gizo na ma'aikatar kasashen waje ta masarautar ya bayyana cewa Abu Dhabi ta fita daga hadakar sojojin ruwa da ke aiki a tekun "Red Sea" da tekun Fasha.

Kamar yadda kafar ta Teghrib News Agency ta ruwaito, masarautar ta yanke shawarar barin hadakar sojojin ruwan ne bayan yin duba a tsanake kan bukatun tsaron ta. 

Masu sharhi kan al'amurra sun bayyana cewa Abu Dhabi ta yanke fitar ne sakamakon fatar da ta ke yi na fadada dangantakar tsaron ta.

No comments

Powered by Blogger.