Header Ads

Ikirarin na bayyana kadarori na naira tiriliyan 9 ba gaskiya ba ne - Gwamnan jihar Zamfara

Sabon gwamnan jihar Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi watsi da ikirarin da ake yi cewa ya bayyana kadarorin da ya mallaka wadanda suka kai naira tiriliyan tara.

Gwamnan a cikin wani jawabi wanda kakakinsa, Sulaiman Idris, ya fitar a ranar Juma'a a Gusau, ya bayyana labarin da kirkirarriyar karya wadda aka shirya domin karkatar da hankalin sabuwar gwamnatin ta Zamfara daga hanyar da ta dauka ta ceto mutanen jihar Zamfara.

Ya kara da cewa cigaba ne da karairayin da wadanda suka fadi zabe suke yi yayin mummunan kamfe din su.

Malam Idris ya bayyana cewa gwamnatin ta fara aiki kuma ta mayar da hankali kan tabbatar da cewa ta kawo tsaftar da ake bukata a gwamnatance a jihar domin ta iya sauke nauyin da ke kan ta.

"Hankalinmu ya karkato kan wani labari mai cutarwa wanda aka kirkiro aka kuma watsa a kafofin sada zumunta da ke ikirarin cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana kadarorin sa da suka kai naira tiriliyan tara. Ya zama dole gwamnatin ta fitar da wannan jawabin domin ana cewa yayin da ake ta maimaita karya (tare da kyale ta ba tare da kalubalantar ta ba) za ta iya dusashe gaskiya. 

"Wannan al'amari na ban dariya da kirkirarriyar karya da aka yi aka watsa a kafofin sada zumunta ba gaskiya ba ne kuma wani wanda wadanda ke da niyyar cutarwa suka yi wanda ke da niyyar karkatar da hankalin sabuwar gwamnati." Kamar yadda ya ke a cikin wani bangaren jawabin.

Kakakin gwamnan wanda ya bayyana a cikin jawabin cewa a doka duka masu ruke da mukaman gwamnati wadanda suka hada da shugaban kasa, mataimakinsa, gwamnoni da duka zababbun jami'ai da ma'aikatan gwamnati sai sun cika tare da bayar da takardar bayyana kadarori, shima gwamna Lawal Dauda ya yi hakan kuma suna tare da hukumar "Code of Conduct Bureau" wadda ke da alhakin hakan.
 
Ya ma kara da cewa hankulansu ba za su karkata kan wadannan kirkirarrun rubuce-rubuce na kafofin sada zumunta ba da aka yi domin jan hankula, domin "Gwamnatinmu ta mayar da hankalinta ne wajen warware matsalolin da suka shafi tsaro, ilimi, tsaftataccen ruwan sha, lafiya, aikin gona da sauran matsalolin da suka shafi al'umma da tattalin arziki da suka shafi jihar. Muna ma aiki ba dare ba rana domin tattabar da cewa mun sauke nauyi tare da yin ayyukan da aka rantsar da gwamna domin ya yi." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

No comments

Powered by Blogger.