Header Ads

Hukumar kashe gobara ta ƙasa ta kare rayukan mutane 2,322, kadarori na naira tiriliyan 25 a cikin shekaru 8 - FFS

Wasu motocin kashe gobara

Hukumar kashe gobara ta gwamnatin tarayya (FFS) ta bayyana cewa ta kare rayukan mutane 2,322 da kadarorin da kudinsu ya kai naira tiriliyan 25.741 a gobarar da aka yi daga shekarar 2015 zuwa watan Maci na 2023.

Wannan na cikin kididdigar hukumar ne na "National Fire Statistics" wadda kakakin hukumar, Mr Paul Abraham, ya sawa hannu a ranar Lahadi a Abuja. 

Kididdigar alkaluman ta nuna cewa hukumar ta samu kira domin a kashe gobara har sau 12,471 a cikin lokacin da ta fitar da bayanin.

Kididdigar ta nuna cewa hukumar ta samu kira domin a kashe gobara 3,555 a shekarar 2020; sai mai bi ma ta shekarar 2022 mai 2,860 da 2,825 a 2021 na kira domin kashe gobara. 

"An lissafo kiran da aka yi domin a kashe gobara 698 a shekarar 2019; 531 a shekarar 2015; 478 a shekarar 2018 da 400 a shekarar 2017 sai kuma kira 391 da aka samu a shekarar 2016." Kamar yadda ta bayyana.

Takardar kididdigar ta nuna cewa an ceto rayuka mafi yawa a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2022 idan aka kwatanta da yawan na shekarun tsakanin 2015 zuwa 2018.

Kamar yadda ya ke a cikin jawabin hukumar, shekarar 2020 ce ta fi kowacce shekara yawan mutanen da aka ceto rayukansu inda ta ke da rayuka 1,100, inda ta kuma bayyana cewa an ceto rayukan mutane 49 daga watan Janairu zuwa Maci na shekarar 2023.

"Hukumar ta ceto kadarori da kudinsu ya kai naira biliyan 593.9 a shekarar 2020; naira biliyan 426.5 a shekarar 2017; naira biliyan 273.12 shekarar 2015 da biliyan 57.5 a shekarar 2016 sai kuma kadara ta naira biliyan 16.1 da aka tseratar daga watan Janairu zuwa watan Maci na shekarar 2023."

Hukumar ta FFS ta ma samar tare da rarraba sabbin motocin kashe gobara 106 kuma ta dauki ma'aikata 2,500 domin taimakawa karfin aikin ta.

"Karin iya ceto rayukan mutane da aka samu a tsakanin shekarun 2019 zuwa yanzu za a iya dangantashi da karin samar da kayayyaki na motar kashe gobara da daukar ma'aikata." Kamar yadda ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.