Header Ads

Hamas ta yi Allah wadai da yunkurin da Isra'ila ke yi na ta rinka sa ƙananan yara Falasɗinawa a kurkuku

Kurkukun Eshel da ke ƙasar Isra'ila

Kungiyar fafutikar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah wadai da yunkurin da gwamnatin Isra'ila ke yi na ta amince da wani kuduri na rinka yanke hukuncin zaman kurkuku ga kananan yaran Falasdinawa masu shekaru 12 ko wadanda suka dara haka.

Kungiyar a cikin wani jawabi a ranar Asabar ta bayyana cewa kudurin, "na yin nuni ne da irin wariya ta gwamnatin da kuma yanayin ta na rashin tausayi."

Kungiyar ta Hamas ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan da suka dace kan Isra'ila sakamakon laifuffukan ta ga yaran Falasdinawa.

"Yaran Falasdinawa a kodayaushe suna fuskantar laifuffuka mafi muni daga zalunci da ta'addancin Isra'ila, wanda ya hada da kisa, kamu, cin zarafi da horo." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

A ranar Lahadi, kwamitin ministoci da ke kula
 da al'amurran dokoki na majalisar Isra'ila ta Knesset ake sa ran za ta tattauna a kan kudirin wanda Yitzhak Kreuzer na jam'iyyar Otzma Yehudit ya shigar. Kudirin ya bayar da dama a sa yara masu kananan shekaru da aka ambata a sama kurkuku a kan caje-cajen da suka hada da mayar da martani a yankin da aka mamaye na al-Quds.

A ranar 28 ga watan Janairu, an yi ikirarin cewa wani matashin Falasdinawa ya harbi wani sojan Isra'ila da ba kan aiki ya ke ba da mahaifinsa tare da yi masa mummunan rauni a al-Quds a farkon shekarar nan. Muhammad Aliwat, mai shekaru goma sha uku daga Silwan, ya bude wuta a kan wani rukunin yahudawa yan-kama-wuri-zauna a kan titin Ma'alot Ir David, a wajen tsohon birnin al-Quds.

Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, wanda soja ne wanda ake sakowa daga jirgin sama ta "Parachute", an yi ikirarin cewa ya samu ya harbi maharin duk da raunin da ya samu. An raunata Aliwat tare da kama shi.

An dai ruwaito cewa akwai sama da Falasdinawa 7,000 a cikin kurkukun Isra'ila. Daruruwan 'yan kurkukun ana tsare da su ne a karkashin ikirarin tsarewar mulki, ba tare da shari'a ba, ba tare da caji ba. Falasdinawa 'yan kurkuku a lokuta da dama sukan yi yajin cin abinci a bayyane domin nuna rashin amincewar su da kama su ba bisa ka'ida ba.

Hukumomin Isra'ila na ajiye Falasdinawa a cikin yanayi mara kyau a kurkuku ba tare da cikakkiyar tsafta kamar yadda ake bukata ba. Falasdinawa da ke kurkukun kan ma fuskanci horo, tursasawa da hana walwala.

Kungiyoyin kare hakkin bil-adama sun bayyana cewa Isra'ila na cigaba da keta duk wasu hakkoki da 'yanci da 'yan kurkuku ke da shi a " Fourth Geneva Convention" da kuma dokokin kasa-da-kasa.

Kamar yadda cibiyar bincike kan 'yan kurkuku ta Falasdinawa ta "Palestine Detainees Studies Center" ta bayyana, akalla kashi 60 na Falasdinawa da ke kurkukun Isra'ila suna fama da cututtuka masu karfi, inda da dama suka rasu yayin da suke a tsare ko bayan an sake su saboda yadda halin da suke ciki ya ta'azzara.

No comments

Powered by Blogger.