Header Ads

Falasɗinawa sun cimma yarjejeniya kan buƙatar wasu ƙungiyoyin Isra'ila na rushe kubbar masallacin Al-Rahman

Masallacin Al-Rahman da ke Beit Safafa a kudu-maso-yammacin Jerusalem

Musulman da ke zaune a wani gari a Jerusalem sun cimma yarjejeniya domin samun mafita dangane da matsi daga rukunin yahudawa yan-kama-wuri-zauna da wasu kungiyoyinsu na rushe wata sananniyar kubba mai kalar zinariya ta masallaci.

Jami'an yankin daga farko sun nemi a cire ginin ne daga masallacin na Al-Rahman da ke Beit Safafa amma bayan an gudanar da wakilanci a bisa doka da tattaunawa da mazaunan yankin an amince cewa a ragewa kubbar tsawo kuma a canza kalarta zuwa mai kalar azurfa. 

A ranar Talata, aikin canzawar, wanda mutanen gari ne ke yi, na cigaba inda zai hada da gina hasumiya.

Beit Safafa Mukhtar, Mohammed Elayan, ya bayyanawa kafar sadarwa ta Arab News cewa: "Mutanen kauyen suna ganin wannan zabin shine wanda ya fi kuma wanda ya fi rashin cutarwa domin a kare masallacin Al-Rahman." 

A shekarar 2021, kwamitin masallacin na Al-Rahman sun kaddamar da kamfe domin tara kudi saboda kara fadin masallacin sun kuma nemi yankin da ya ba su izini.

Sai dai shirin ya bata ran yahudawa yan-kama-wuri-zauna wadanda suka yi ikirarin cewa kubbar mai kalar zinariya ta yi kama da ta "Dome of the Rock" tare da yin kira da a rushe ta, cewa an gina ta ne ba tare da umarni ba.

Elayan ya bayyana cewa: "Wannan al'amarin ya bata ran yahudawan 'yan-kama-wuri-zauna, musamman saboda masallacin na da girma kuma da fadi, kuma kubbar na da tsawo kuma ana iya ganinta daga ko'ina. Yana a wajen kauyen ne kuma a zagaye da rukunin masana'antun Isra'ila." 

Ya bayyana cewa yahudawan 'yan-kama-wuri-zauna sun bayyana ikirarin nasu ne ta hanyar daukar hotuna da bidiyoyi da tura labaru na kai tsaye a kusa da masallacin a kafofin sada zumunta.

"'Yan kwanaki kadan bayan nan, hukumar yankin ta zo wurin domin ta ji me ke faruwa, wanda hakan ya sa magajin garin suka hadu, suka bibiyi yadda al'amurra ke tafiya tare da cimma matsaya a kan ka'ida domin gujewa duk wani abu na rushe masallacin." Kamar yadda ya bayyana.

Beit Safafa gari ne na Falasdinawa da ke a kilomita 4 daga kudu-maso-yammacin Jerusalem kuma a arewacin Bethlehem, wanda ke da yawan mutane 18,000. Yana zagaye ne da gine-ginen Isra'ila kuma hukumomin Isra'ila sun kwashi filin kasa domin aikin gine-gine.

No comments

Powered by Blogger.