Header Ads

Dubunnan mutane sun yi zanga-zanga a Faransa kan shirye-shiryen gwamnatin ƙasar

Dubunnan mutane a kasar Faransa sun gabatar da sabbin zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu ga shirye-shiryen gwamnati na yin duba ga fansho tare da kara shekarun yin ritaya zuwa 64.

Kungiyoyin ma'aikatan Faransa ne suka shirya zanga-zangar da aka ya a ranar Talata, a matsayin rana ta 14 da ake zanga-zanga domin nuna kin amincewa da yunkurin gwamnati na kara shekarun ritaya.

Kamar yadda hukumomi suka bayyana, tsakanin mutane 400,000 zuwa 600,000 ake sa ran za su fito wajen gudanar da zanga-zangar a ranar Talata a fadin kasar Faransa.

Rikici ya barke ma a tsakanin masu zanga-zangar da 'yan sanda a Nantes yayin da zanga-zanga ta keta ta cikin birnin da ke yammacin kasar Faransa, inda suke wurga abubuwa ga 'yan sandan su kuma suna harbo masu barkonun tsohuwa (tear gas).

Mambobin kungiyar ma'aitaka wadda ta fi tsatstsauran ra'ayi ta CGT sun mamaye cibiyar Paris Summer 2014 Olympics na dan wani lokaci. Hotunan da gidan talabijin din BFM ya nuna sun nuno masu zanga-zangar na shiga ginin wanda ke Aubervilliers a arewacin Faransa.

"Da dama daga cikin 'yan kungiyar ta CGT sun shiga ginin na 'yan mintoci domin ajiye alluna na nuna rashin amincewa da sauye-sauyen. Ba a yi rikici ba kuma ba a lalata kayayyaki ba." Wani kakakin wasanni ya shaidawa kafar watsa labaru ta Reuters.

A wasu wuraren masu zanga-zanga sun dakko tutoci tare da alluna inda suke kira ga Macron da ya dakatar da canje-canjen na dole.

Wadanda suka shirya zanga-zangar na fatar cewa zanga-zangar ta kara sa matsi ga 'yan majalisar dokoki su sake yin duba ga canje-canjen fansho din tare da gudanar da zabe a kan sa.

A yayin da ake tsaka da hakan, jami'an tsaron Faransa sun samar da 'yan sanda 11,000 a fadin kasar a ranar Talata.

A Paris, 'yan sanda sun tsaya a wajen majalisar kasar, inda suka rufe babbar hanyar da ake bi a shiga tare da binciken wadanda ke wucewa a babban birnin kasar ta Faransa.

Sai dai shugaban kasar, Emmanuel Macron, ya yi ikirarin cewa ya ji muryoyin mutane da suka fusata sakamakon kara shekarun yin ritayar daga 62 zuwa 64, sai dai ya kafe cewa ana bukatar yin hakan domin yanayin fansho din ya kasance yana tafiya daidai a yayin da mutanen kasar ke kara shekaru.

No comments

Powered by Blogger.