Header Ads

Dubban mutane na neman muhalli, wasu 19 sun rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ke haɗe da iska a kudancin Asia

Wasu mutane na amfani da dan karamin jirgin ruwa bayan an yi ruwan sama mai hade da iska a kauyen Kenduguri da ke jihar Assam a kasar Indiya a ranar 23 ga watan Yuni, 2023.

Akalla mutane 19 suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa biyo bayan iska mai karfi da kan faru a duk shekara a kudancin Asia, hade da mako wanda aka samu ruwan sama akai-akai da ya tilastawa dubunnan mutane neman muhalli a Indiya.

An saba ganin ambaliyar ruwan kuma yana haifar da asarori mai yawa yayin lokacin iskar, amma masana sun bayyana cewa canjin yanayi na kara yawansa, muninsa da rashin tabbacin lokacin faruwarsa. 

Kididdigar daga ambaliyar ruwan da kuma zaizayewar kasar a ranar Juma'a ta karu zuwa 14 a ranar Juma'a, inda da dama kuma har yanzu ba a gansu ba kamar yadda jami'ai suka bayyana.

"Masu bincike da aikin ceto har yanzu suna kan aiki." Kamar yadda kakakin hukumar kula da annoba ta kasar, Druhba Bahadur Khadka, ya shaidawa kafar watsa labaru ta AFP a ranar Juma'a.

Wasu hudu kuma sun rasa rayukansu a ambaliyar ruwa da zaizayar kasa a jihar Himalayan ta Arunachal Pradesh da ke kusa da kan iyakar kasar Sin, kamar yadda hukumar kula da annobar ta bayyana a ranar Alhamis.

Hukumomi a makwaftan jihar sun ce mutum daya ya rasa ransa a ruwan ambaliya da yammacin ranar Alhamis yayin da ruwa ya shanye kauyuka sama da 1,300.

Kusan mutane 14,000 ne suka bar gidajensu zuwa muhallan gaggawa, kamar yadda hukumar kula da annobar ta Assam ta kara da bayyanawa.

Kasar Bangladesh ita ma tana a shirye bayan da masu hasashe suka yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a yankunan arewaci da ke da iyaka da Indiya.

Akalla iyalai 20,000 ne ambaliyar ruwan ta shafa a yankunan da ke cikin kwari kawo yanzu a arewacin yankin Kurigram, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

"Manyan rafuka a yankin na kara cika." Mohammad Rezaul Karin, wanda shine shugaban yankin, ya shaidawa AFP. "Yanayin zai kara muni idan yawan ruwan da ke zuwa ya karu." 

Iskar Asia da ke zuwa a wannan lokacin iska ce mai karfi da a sanadiyyar ta kudancin Asia ke samun kashi 70 zuwa 80 na ruwan sama a shekara da ke fara zubowa a tsakanin watan Yuni da Satumba a kowacce shekara, kamar yadda kafar watsa labaru ta Channels ta ruwaito. 

Tana da matukar amfani ga noma saboda haka ga rayuwar miliyoyin manoma da tabbatar da isasshen abinci a yankin da ke da kusan mutane biliyan biyu.

Sai dai, ta kan haifar da asarori a zaizayar kasa da ambaliyar ruwa.

A shekarar da ta gabata, ambaliyar ruwa da ke hade da iska ta sa kashi uku na kasar Pakistan a karkashin ruwa, inda ta lalata gidaje miliyan biyu tare da sanadiyyar rasa rayukan mutane 1,700.

Bangladesh ita ma ta fuskanci ambaliyar a shekarar wadda ta yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 100 tare da hana mutane miliyan bakwai gudanar da ayyukansu na yau da kullum kamar yadda aka saba.

No comments

Powered by Blogger.