Header Ads

Ƙasashe sun yi Allah wadai da keta alfarmar Al-Qur'ani da wasu Yahudun Isra'ila suka yi

Alkur'ani mai tsarki

Kungiyoyin Falasdinawa da kasashe a yankuna na duniya sun yi Allah wadai da keta alfarmar masallaci da kuma Al-Qur'ani da wasu yahudawa yan-kama-wuri-zauna masu tsatstsauran ra'ayi suka yi yayin wani hari da suka kai ranar Laraba a wani kauye da ke Gabar yamma da kogin Jordan da aka mamaye.

Sabon bidiyon kyamarar CCTV da aka fitar ya nuna rukunin yahudawa yan-kama-wuri-zauna sun afka kauyen Falasdinawa na Urif da ke kudancin Nablus tare da shiga wani masallaci inda suka lalata kayan da ke ciki, tare kuma da daukar kwafin littafin Al-Qur'ani inda suka yayyaga shafukansa kafin daga bisani suka wurga littafin mai tsarki a kan titi.

Hazem Qassem, kakakin kungiyar fafutika ta Hamas, a ranar Juma'a ya bayyana cewa abinda ya faru a kauyen Urif mummunan laifi ne kuma yana iya tunzura yakin addini wanda Isra'ila ta kaddamar.

Qassem ya bayyana cewa wannan mummunar dabi'a ta yahudawa yan-kama-wuri-zaunan wadda sojojin mamayar suke goyon baya cin mutunci ne ga baki daya mutanen Falasdinawa kuma nuna ko in kula ne ga abubuwan su masu tsarki da bai taba faruwa ba a baya.

Kakakin ya yi kira ga kasashen musulmai da kungiyoyin musulmai da su fitar da matsaya bayyananniya a kan al'amarin wanda ya bayyana da "mummunar dabi'ar nuna wariya."

Kakakin ya bayyana cewa gwamnatin mamaya ta Isra'ila da yahudawa yan-kama-wuri-zauna sune ke da cikakken alhakin duk wani abu da zai biyo baya sakamakon yakin addini da suke kaddamarwa a kan wurare masu tsarki na musulmai, kuma cewa sai sun girbi abinda suka shuka sakamakon wannan laifin da zaluncin a kan Falasdinawa.

A bangare daya kuma, kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad a ranar Juma'a a cikin wani jawabi ta bayyana cewa harin na yahudawa yan-kama-wuri-zauna gwamnatin Isra'ila ce ta tunzura shi, inda ta bayyana cewa gwamnatin ce ke da cikakken alhakin sakamakon hakan da zai biyo baya.

Kungiyar ta ma sha alwashin mayar da martanin Falasdinawa ga wannan irin laifi.

Ma'aikatar Harkokin Kasashen Turkiyya ta yi Allah wadai da harin a matsayin harin kiyayya da ba za a amince da shi ba, inda ta yi kira da a dauki mataki a kan wadanda suke da alhakin hakan.

Bayan haka, Ma'aikatar da ke kula da al'amurran addini ta kasar Misra ta yi Allah wadai da keta alfarmar Al-Qur'ani inda ta bayyana hakan da "ta'addanci, tsatstsauran ra'ayi da kuma nuna wariya." 

Hare-haren na ranar Laraba na zuwa ne kwana daya bayan kashe wasu yahudawa yan-kama-wuri-zauna hudu da kuma raunata wasu hudu a yayin wani hari na harbi da Falasdinawa masu fafutika biyu suka kai a wata tashar gas a wajen gine-ginen Eli da ba kan ka'ida suke ba a yankin da aka mamaye na gabar yamma da kogin Jordan, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

Wadanda suka kai harin, wadanda sojojin Isra'ila suka bayyana da mazaunan kauyen Urif ne, an harbe su inda aka kashe su.

Arewacin Gabar yamma da kogin Jordan ya kasance waje da ake ta samun hare-haren Isra'ila da na yahudawa yan-kama-wuri-zauna a kan al'ummar Falasdinawa a satin da ya gabata.

Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna sun kutsa garuruwan Falasdinawa da ke Gabar yamma da kogin Jordan a daren ranar Talata inda suka kona motoci, suka kona gonaki tare da lalata gidaje, wani yanayi da ya yi kama da kisan kiyashi na farkon shekarar nan a kauyen Huwara.

A ranar Litinin, wata babbar tawagar sojojin Isra'ila da suka kutsa sansanin 'yan gudun hijira na Jenin ta yi sanadiyyar rasuwar mutane bakwai, ciki har da 'yan shekaru 15. Akalla mutane 91 suka raunata yayin kutsen da suka yi na tsawon awa tara. 

A fito-na-fito din an ga Isra'ila ta yi amfani da bindigogin jirgi mai saukar ungulu (Helicopter) a karon farko a cikin shekaru da dama a Gabar yamma da kogin Jordan, yayin da su kuma mayakan Falasdinawa suka sa wani babban bam na gefen hanya a kasan wata motar yaki ta Isra'ila.

Akalla Falasdinawa 170 sojojin Isra'ila da yahudawa yan-kama-wuri-zauna suka kashe tun farkon wannan shekarar.

No comments

Powered by Blogger.