Header Ads

An yi babbar arangama a babban birnin Sudan bayan tsagaita wutar awowi 24 ta zo karshe

Hayaki ya turnuke sararin samaniyar Khartoum Sudan

Babban birnin kasar Sudan da sauran wuraren da ke kusa da shi sun kasance wasu wurare da ke fuskantar arangama mai karfi bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta awowi 24 a tsakanin sojojin kasar da dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF) ta zo karshe.

A ranar Lahadi, rikicin ya barke a Khartoum da kuma sauran biranen Bahri da Omdurman wadanda suka hada babban birnin kasar da ke arewacin nahiyar Afirka a kusa da River Nile.

Shaidun sun bayyana sabbin arangamar a matsayin wadanda suka fi tsanani tun bayan da fada ya barke a ranar 15 ga watan Afirilu, lokacin da bangarorin sojoji da ba su shiri da juna suka fara fada domin neman iko tsakanin shugaban sojoji Janar Abdel Fattah al-Burhan, da tsohon mataimakinsa, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda shine shugaban RSF.

A cikin baki daya fadan da ake yi, sojojin na kai hare-hare ta jiragen yaki ne a kan RFS, wadda ita kuma mafiyawanci ke ramuwa da bindigogin harbo jirgi.

 "Yarjejeniyar ta sa mun dan samu natsuwa, amma yakin da tsoron na dawowa a yau." Kamar yadda Reuters ta ruwaito wani shaida na fadi.

Kamar yadda wani mai fafutika ya bayyana, akalla fararen hula 11 suka rasa rayukansu a wurare biyu da aka harba manyan bindigogi a kudancin Khartoum, yayin da kuma fararen hula shida suka rasa rayukansu a arewacin Khartoum.

Daruruwan mutane sun rasa rayukansu tun bayan barkewa fada a tsakanin sojojin da RSF inda kuma mutane sama da miliyan 1.9 suka bar muhallansu, wanda hakan ke barazana ga yanayin rayuwa da ke neman yaduwa a yankin baki daya. 

Wasu mutane 400,000 da suka bar muhallansu sun shiga kasashe ne makwafta, kuma kusan rabin su sun nufi arewacin Misra ne.

A ranar Asabar, Kasar ta Misra ta kara tsaurara dokokin shiga kasar inda ta kara tsawaita bukatar biza ga duka maza da suke tsakanin shekaru 16 zuwa 50 'yan kasar Sudan.

Saudi Arabiya da Amurka wadanda sune suka shiga tsakani a yarjejeniya da aka yi da dama a tsakanin bangarorin da ke fada da juna, sun yi Allah wadai da dawowar rikicin.

A cikin wani jawabi na hadaka, masu shiga tsakanin sun bayyana cewa sojojin da RSF sun iya samu sun killace mayakansu yayin tsagaita wutar, inda suka kara da cewa Riyadh da Washington sun "Ba su ji dadi ba sakamakon dawowar fadan nan-da-nan."

No comments

Powered by Blogger.