Header Ads

Amurka za ta aika da makamai da kudinsu ya kai dala miliyan 325 zuwa Ukraine

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden tare da shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky

Amurka ta bayyana cewa za ta sake tura wani sabon taimakon soji na dala miliyan 325 wanda ke nuni da watsi da gargadin da Rasha ta sha yi.

A ranar Talata Pentagon ta bayyana cewa taimakon zai hada ne da makaman tsaron sararin samaniya, makamai wadanda ake harbawa da motoci.

Sanarwar na zuwa ne a yayin da kasar Rasha ta saki wani sabon bidiyo da ke nuna rundunar sojojin Rasha na duba tankokin da Jamus ta kera na Leopard da kuma motocin Amurka na Bradley a Ukraine wadanda ta kama. 

Wannan dai shine taimako na 40 da aka yi gaggawar kaiwa kasar Ukraine ta hanyar amfani da "Presidential Drawdown Authority" ko DPA, wanda ta hakan shugaban kasar Amurka a kan doka zai iya bayar da umarnin kai makamai ko sauran wasu abubuwan daga ma'ajiyar Amurka ba tare da samun amincewar Congress ba a yayin gaggawa.

Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan Pentagon ta bayyana cewa za ta samar da karin dalar Amurka biliyan 2.1 na taimakon makamai ga Ukraine. 

A ranar Juma'a Pentagon ta bayyana taimakon sojin na tsawon zango ga kasar ta Ukraine zai hada ne da makaman tsaron sararin samaniya da kuma makaman roka, harsasan da ba a bayyana yawansu ba da kuma kudi domin horo da kuma taimakon dawainiya.

Washington ta samar da taimakon tsaro na kusan dala biliyan 38 tun bayan da Rasha ta fara abinda ta kira aikin soji na musamman a kasar a watan Fabrairun 2022.

Duk da cigaba da taimakon Kiev da Washington ke yi, gwamnatin Biden ta bayyana cewa sojojin Amurka ba za su yi yaki da Rasha ba a Ukraine.

Jami'an kasar Rasha sun sha maimaita cewa ambaliyar makamai ga Ukraine zai kara ruruta abubuwa ne.

'Yan majalisar Amurka na jam'iyyar Republican sun nuna damuwarsu kan tura kayayyakin soji ga Ukraine.

Wata 'ya majalisar Amurka, Marjorie Taylor Greene ta ce taimakon da Amurka ke yi ga Ukraine na soji "yaki ne a kaikaice" da Amurka ke jagoranta kan Rasha.

Ta bayyana cewa yakin Ukraine ya dora wani nauyi na kudi kan Amurkawa, wadanda tuni suke fama da talauci.

No comments

Powered by Blogger.