Header Ads

Allah Ya yi wa tsohon Wazirin Kano kuma limamin waje, Sheikh Nasir Muhammad Nasir, rasuwa

Marigayi Sheikh Nasir Muhammad Nasir

Allah Ya yi wa tsohon Wazirin Kano kuma limamin waje, Sheikh Nasir Muhammad Nasir, rasuwa a ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023.

Marigayi Sheikh Nasir shine limamin masallacin wajen kwaryar birnin Kano da ke Fagge, karamar hukumar Fagge da ke jihar Kano.

Sheikh Nasir dai kafin rasuwarsa ya kwashe tsawon shekaru yana koyar da ilimin addinin musulunci a masallacinsa da ke Fagge, kuma marigayin ya kasance Amini ga marigayi sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Za a yi jana'izar marigayin ne a Kofar Kudu, Fadar Mai Martaba Sarkin Kano da misalin karfe 9:00 na safe a ranar Alhamis, 8 ga watan Yunin 2023. 

Allah Ya jikansa da gafara.

No comments

Powered by Blogger.