Header Ads

Alhazan Nijeriya 559 sun tsira da rayukansu bayan da tsawa ta fada kan wani jirgin sama na Max Air

Kimanin alhazan Nijeriya 559 daga jihar Jigawa ne suka tsira da rayukansu cikin sa'a bayan tsawa ta fada a wani jirgin Max Air da zai kai su kasar Saudi Arabiya.

Al'amarin ya faru ne da yammacin ranar Laraba 'yan mintoci bayan jirgin ya tashi daga filin sauka da tashin jiragen sama na Kasa-da-kasa da ke Dutse, babban birnin jihar ta Jigawa.

Jirgin wanda ya bar filin sauka da tashin jiragen sama da ke Dutse da misalin karfe 3:46 na yamma, ya tunkari Jeddah ne da ke Saudi Arabiya.

Hancin jirgin na Max Air, wanda ke da namba Max B747-HMM, ya lalace.

No comments

Powered by Blogger.