Header Ads

A rana ta farko ta taron Larabawa da ƙasar Sin an cimma yarjeniyoyi 30 da kimarsu ta kai dala biliyan 10

Ministan Harkokin Kasashen Wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan al - Saud (a dama) da kuma shugaban taron tuntuba na siyasa na mutanen kasar Sin, Hu Chunhu, a wurin taron kasuwanci na Larabawa da kasar Sin karo na 10 a Riyadh, 11 ga watan Yunin 2023.


A ranar ta farko ta taron kasuwanci a tsakanin Larabawa da kasar Sin karo na 10 an cimma yarjeniyoyin kasuwanci 30 wadanda kimarsu ya kai dala biliyan 10 a bangarori da dama da suka hada da fasaha, sake gyara abubuwan da aka yi amfani da su, aikin gona, gine-gine, ma'adanai, tsarin safarar kayayyaki, yawan bude ido da harkar kula da lafiya.

Kamar yadda ma'aikatar zuba jari ta bayyana, gwamnatin Saudiyya ta sa hannu da kamfanonin kasar Sin daban-daban wadanda suka hada da binciken kere-kere, cigaba, kera kayayyaki da sayarwa, cigaban yawan bude ido da sauran manhajoji da sauransu a masarautar.

An ma sa hannu a cikin yarjeniyo da ke tsakanin kasuwanci zuwa kasuwanci da dama a taron na kasuwanci da aka yi a Riyadh a ranar Lahadi.

Yayin da ya ke jawabi a wajen taron, Ministan Makamashi na kasar Saudiyya, Yarima Abdulaziz bin Salman ya ce, "Ba zan yi mamaki ba in kun sake jin wani labari dangane da sa jari tsakanin Saudiyya da Sin." Inda ya kara da cewa masarautar na neman hada hannu ne da kasar da ke da karfin tattalin arziki na biyu a duniya a maimakon gasa.

Masarautar Saudiyya ce dai ke da kashi 25 na dalar Amurka biliyan 432 na safara a tsarkin kasar Sin da kasashen Larabawa a shekarar 2022.

Yawan safara a tsakanin kasar Sin da Saudi Arabiya ta kai dala biliyan 106 a shekarar 2022, hakan na nufin kari na kashi 30 kan na shekarar 2021.

No comments

Powered by Blogger.