Header Ads

A karon farko Babban Limamin Masallacin Al - Azhar zai yi jawabi ga majalisar dinkin duniya

Babban limamin masallacin Al-Azhar da ke ƙasar Misra, Sheikh Ahmed Al-Tayyeb

Babban shugaban addini na kasar Misra a ranar Laraba zai yi jawabi kan amfanin 'yan uwantakar addini, zama da mutane daban-daban, da girmamawa juna domin samun zaman lafiya a duniya yayin jawabinsa a Kwamitin Tsaro na majalisar dinkin duniya.

Sheikh Ahmed Al-Tayyeb, babban limamin Al-Azhar, zai yi jawabi ne a yayin tattaunawa a kan yadda za a habbaka da kuma tattabar da wanzuwar zaman lafiya a duniya.

A cikin jawabinsa, Al-Tayyeb, wanda shine shugaban majalisar dattawa musulmai (Muslim Council of Elders), zai fi mayar da hankali ne a kan amfanin habaka kyawawan dabi'u da kuma amfaninsu wajen wanzar da sakon zaman lafiya.

A cikin wani jawabi, Al-Azhar Al-Sharif, wanda ya ke wuri ne mafi tsufa kuma cibiyar karatu ta Sunni, ta bayyana tattaunawar da "mai matukar tarihi kuma dama da ba a samu ba" domin rawar da shugabannin addinai za su taka wajen haduwar dabi'u masu kyau na abokantakar 'yan Adam da kuma taimakon juna.

Wannan zai kasance karo na farko da Kwamitin Tsaro na majalisar dinkin duniya ya yi zama wanda ya hada da manyan masu tsara abubuwa, shugabannin siyasa da manyan sanannun mutane a bangaren addini, ciki harda Al-Tayyed da Pope Francis.

A shekarar 2019, shugaban Cocin Roman Katolika da kuma limamin Al-Azhar sun sa hannu a kundin 'Yan uwantakar 'Yan Adam a Abu Dhabi.

A bangare daban kuma, babban malami a Misra, Shawki Allam, shugaban babban kwamiti na babbar sakatariyar hukumomin fatawowi ta duniya, zai kasance wurin taron dinke baraka a tsakanin gabashi da yammaci.

Za a yi taron ne a ranar Laraba a "Trusteeship Council Chamber " a cibiyar majalisar dinkin duniya da ke New York.

Babban mai bayar da shawara ga Allam, Ibrahim Negm, ya bayyana cewa, "Wannan ziyarar ta kwana hudu cigaba ne kan zagayen kasa-da-kasa da babban limamin Misra ke yi wanda ke kan layi da irin shirin da Dar Al-Ifta ke yi a matsayin ta na wata sassaukar hanya ta samar da bayanan da suka shafi sadarwa a addini da kuma zuwa bangarori na duniya." 

Ziyarar babban malamin, kamar yadda ya kara da bayyanawa, zai hada da tattaunawa da shugabannin majalisar dinkin duniya, "Domin kara karfin sadarwa da hadin kai da kuma tarurruka wadanda za su habaka al'adar sadarwa, fahimta da kuma koyar da ilimi. Wanna mataki ne domin kare martabar Musulunci a kasashen yamma da kuma tunkarar kiyayya ga addinin musulunci, kalaman batanci da kuma tsatstsauran ra'ayi."

No comments

Powered by Blogger.