Header Ads

Zuwa yanzu Isra'ila ta kashe Falasdinawa 160 a cikin wannan shekarar - ma'aikatar lafiya ta Falasdinu

Masu makoki sun dakko Falasdinawa da sojojin Isra'ila suka kashe sakamakon wani kutse da suka yi a birnin da ke yamma da gabar kogin Jordan na Jenin a ranar 26 ga watan Janairu na shekarar 2023.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 160, ciki har da mata da yara tun shigowar wannan shekarar ta 2023, kamar yadda ma'aikatar lafiya ta Falasdinawa ta bayyana a ranar Litinin.

Kamar yadda ma'aikatar ta bayyana, Falasdinawa 36 aka kashe a yankin zirin Gaza, 120 a yankin da aka mamaye na yamma da gabar kogin Jordan sai kuma hudu da aka kashe a cikin Isra'ila.

A farkon wannan watan, Isra'ila ta kammala kai hare-hare na tsawon kwanaki biyar a Gaza, sakamakon haka ta kashe mutane 33, ciki da mata uku da yara shida.

Kutsowa da Isra'ila ke yi cikin garuruwa da biranen Falasdinawa da ke yamma da gabar kogin Jordan ya kasance wani al'amari da ke faruwa a kusan kowanne dare kuma sanadiyya ta mafi yawan rayukan da aka rasa. Wannan kuma na hade da keta alfarmar masallacin al-Aqsa a kullum da kuma tsagaita tafiye-tafiye da aka kakaba kan Falasdinawa da ke zaune a yankunan da aka mamaye.

No comments

Powered by Blogger.