Header Ads

Za a yi amfani da kujeri masu tarihi wajen nadin sarautar Sarki Charles na Ingila

Sarkin Ingila, Charles Philip Arthur George da matarsa Camilla Parker Bowles

Fadar Buckingham na cigaba da bayyana yadda nadin sarautar sarki Charles za ta kasance a ranar Asabar mai zuwa, inda ta bayyana cewa za a yi amfani da kujeru masu tarihi yayin nadin sarautar.

Kujera mai dadadden tarihi ta St. Edward wadda ke da shekaru sama da 700 kuma farkon amfani da ita shine yayin nadin sarautar Sarki Edward II a shekarar 1308, za a yi amfani da ita a yayin nadin sarautar Sarki Charles, kamar yadda Al-Rai daily ta ruwaito daga Reuters.

Bayan haka, fadar ta bayyana cewa sarkin da matarsa Camilla za su zauna yayin gudanar da abubuwa daban-daban yayin nadin a kan wasu kujerun masu tarihi.

Fadar ta kara da cewa kujerun da za a yi amfani da su a farkon bikin da kuma wadanda za a yi amfani da su yayin nadin Camilla an yi su ne domin nadin sarautar mahaifiyar Charles, Sarauniya Elizabeth, a shekarar 1953.

Bayan haka, Charles da Camilla za su zauna a kan karaga a yayin wani bangare na bikin nadin sarautar.

Kujerun guda biyu an yi su ne domin nadin sarautar Sarki George VI, da matarsa, Sarauniya Elizabeth, wadda daga baya aka fi sani da "the Queen Mother" a shekarar 1937. Fadar ta bayyana cewa kujerun na sarauta "An gyara su kuma an sanya su yadda suka fi dacewa kamar yadda ake bukata."

No comments

Powered by Blogger.