Header Ads

Za a buɗe masallacin sallar Juma'a na farko a majalisar wakilai ta Nijeriya

Masallacin sallar Juma'a da za a bude a majalisar wakilai ta Nijeriya

A karon farko tun kafuwar majalisar wakilai ta kasa a Abuja, an gina tare da samar da masallaci domin gudanar da salloli na kowacce rana da kuma sallar Juma'a wanda za a bude a ranar Juma'a 2 ga watan Yuni na shekarar 2023.

A yayin da ya ke rantsar da kwamitin mutane 7 wadanda za su yi aikin tsare-tsare a ofishin sa, shugaban kwamitin ginin masallacin Sanata Ibrahim Shekara ya nemi mambobin kwamitin da su yi aiki sosai domin tabbatar da bude masallacin cikin nasara ba tare da wata matsala ba.

A yayin da ya ke jawabi a madadin mambobin kwamitin, shugaba kuma mamba a majalisar wakilai ta kasa, Honorabul Injiniya Yunusa Abubakar, ya tabbatar da cewa mambobin kwamitin suna iyakar kokarinsu tare da yin godiya ga Allah da Ya nufa suka kasance cikin wadanda ke yin wannan aiki wanda ya ke kyakkyawa.

Injiniya Yunusa Abubakar ya ma nemi mambobin da su kasance masu sadaukarwa sakamakon karancin lokacin aikin nasu.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da zababben sanata Honorabul Nasiru Sani Zagon Daura, Honorabul Isiyaka Ibrahim, Ustaz Sadiq Bala Illelah, Pharm Mustafa Muhammad, Dakta Sule Ya'u Sule a yayin da Haruna Ibrahim Shekarau shi zai yi aiki ne a matsayin sakataren kwamitin.

No comments

Powered by Blogger.