Header Ads

Yanzu Covid-19 ba al'amarin gaggawa ba ne da ya shafi ɓangaren lafiya a duniya - hukumar WHO

Shugaban hukumar lafiya ta duniya, Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa yanzu Covid-19 ba al'amarin "gaggawa bane a bangaren lafiya a duniya."

Jawabin na zuwa ne a matsayin wani babban mataki da aka dauka domin kawo karshen annobar kuma yana zuwa ne shekaru uku bayan an yi babban gargadi a kan kwayar cutar.

Jami'ai sun bayyana cewa yawan wadanda suke mutuwa sakamakon cutar ya ragu daga kololuwarsa na mutane 100,000 a sati a cikin watan Janairun shekarar 2021 zuwa kadan a kan 3,500 a ranar 24 ga watan Afirilu.

Shugaban hukumar ta WHO, Dakta Tedros Adhanom Gebrehyesus, ya bayyana cewa mutane miliyan bakwai ne suka rasu sakamakon annobar.

Inda ya bayyana cewa kididdigar ta gaskiya ta wadanda suka rasu za ta iya kaiwa kusan miliyan 20 - kusan ya lunka kiyasin da aka yi a hukumance sau uku - kuma ya yi gargadin cewa kwayar cutar har yanzu barazana ce.

"A jiya, kwamitin gaggawa sun same ni karo na 15 kuma sun neme ni da bayyana kawo karshen wannan matsala ta kasa baki daya da ta shafi duniya. Na kuma yarda da shawarar. Saboda haka cike da fata mai girma, ina bayyana cewa Covid-19 ba al'amarin lafiya na gaggawa bane da ya shafi duniya." Kamar yadda Dakta Tedros ya bayyana.

Ya kara da cewa daukar matakin da aka yi an yi tunaninsa a hankali na tsawon lokaci kuma an zartar da shi ne a kan kula da bayanai a cikin natsuwa.

Sai dai ya yi gargadin cewa cire babban gargadin da aka yi ba yana nufin hatsarin ya tafi ba ne inda ya bayyana cewa za a iya maido da yanayin gaggawa in har halin da ake ciki ya canza.

"Mafi munin abinda wata kasa za ta yi shine ta yi amfani da wannan labarin wajen cire matakan kariyar ta, ta lalata shirye-shiryen da ta yi, ko kuma ta turawa 'yan kasarta sakon cewa Covid-19 yanzu ba wani abu bane da za a damu da shi." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.