Header Ads

'Yan sandan jihar Kano sun cafke matar da caka wa wata yarinya wuka a ciki

Matar da ta yi kisan tare da wukar

'Yan sanda a jihar Kano sun kama wata mai suna Fatima Salisu mai shekaru 35 da ke zaune a Gadon Kaya Quarters a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano sakamakon yunkurin kisan kai da haifar da munanan raunuka ga wata yarinya 'yar shekara 8 mai suna Sharifa Usman.

A dai ranar ta 14 ga watan Mayu na wannan shekara ne da misalin karfe 6:40 na yamma wani mutum ya kira 'yan sandan a waya domin kawo dauki wanda a kiran ya yi rahoton cewa ya ji karar wata yarinya daga cikin wani gini wanda ba a kammala ba da ke Kureken Sani a karamar hukumar Kumbotso da ke jihar Kano. Sakamakon haka, ya je wurin inda kuma ya tarar da yarinya kwance cikin jini an kuma yanke ta da wuka kuma wukar na kafe a cikinta, bayan wasu raunukan da ta samu a wasu sasssan jikinta.

 Bayan samun wannan rahoto ne aka gaggauta tafiya da yarinyar asibitin Aminu Kano Specialist Hospital inda aka kwantar da ita, kuma nan take kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, pcs ya bayar da umarni ga 'yan sanda baki dayansu da su yi amfani da duk wani abu da suka mallaka domin tattabar da cewa wanda ko wadanda suka aiwatar da wannan al'amari sun fuskanci hukunci.

Bayan farfadowar Sharifa Usman, wadda ke zaune a Gadon Kaya Quarters da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano, ta bayyana cewa wata mata makwafciyar su wadda ta bayyana da Fatima ce ta dauke ta daga Gadon Kaya Quaters zuwa ginin wanda ba a kammala ba da ke Kureken Sani a karamar hukumar Kumbotso tare da yankan ta da wuka a wuya, ciki tare da kuma barin wukar a cikin na ta sannan ta gudu daga wurin da al'amarin ya faru.

A dai farkon fara bincike, 'yan sandan sun kama mijin Fatima Salisu mai suna Yusuf Aminu, wanda mazaunin Gadon Kaya Quarters ne da ke karamar hukumar ta Gwale a jihar Kano. Mijin ya yi ikirarin cewa akwai hujjojin rashin lafiyar kwakwalwa a tattare da matarsa kuma bai san inda ta ke ba. Sai dai yayin da aka cigaba da bincike da tattaro bayanai an kama wadda ake zargin aikata laifin 'yar shekara 35 a wani wuri da ta je ta boye a kauyen Dungulmi da ke yankin Isari a karamar hukumar Dutse da ke jihar Jigawa a ranar 18 ga watan Mayu na shekarar 2023.

A yanzu haka ana gudanar da bincike a kan wadda ake zargin a sashen 'yan sanda na binciken laifuffuka (CID) a bangaren da ke bincike kan kisan kai. 

Wadda ake zargin ta amsa laifin ta, inda kuma ta bayyana cewa ta yi hakan ne domin daukar fansa saboda mahaifin yarinyar na ba mijinta shawarar ya karo mata ta biyu.

To sai dai binciken da ake gudanarwa na neman amsoshin wasu tambayoyi domin gano hakikanin me kenan a cikin laifin da aka aikata sakamakon jawabin da mijin ta ya yi tun a farko, tambayoyin kuwa sune:

i. Me ya sa wadda ake zargin ta dauki yarinyar daga Rijiyar Zaki da ke karamar hukumar Gwale ta kai ta Kureken Sani Quarters da ke karamar hukumar Kumbotso?

ii. Me ya sa wadda ake zargin ta kai yarinyar ginin da ba a kammala ba kebantacce wanda ya ke can nesa?

iii. Me ya sa wadda ake zargin ta gudu zuwa waje mai nisa (jihar Jigawa) bayan ta aikata laifin?

iv. Me ya sa wadda ake zargin ta ki bayyana inda ta ke ga mijin ta, yaran ta da sauran 'yan uwanta bayan ta gudu daga wurin da aka aikata laifin?

A yayin da ake addu'o'in samun lafiya ga Sharifa Usman sakamakon raunukan da ke jikinta, kwamishinan 'yan sandan ya nuna godiyarsa ga wadanda suka taimaka da bayanai wadanda suka yi sanadiyyar kama wadda ake zargin. Za a kai al'amarin kotu bayan kammala bincike.

No comments

Powered by Blogger.