Header Ads

'Yan sanda sun yi nasarar hana wani mai talla Rabiu Nafiu fadawa cikin teku a Legas

Rabi'u Nafi'u

Da safiyar ranar Talata, jami'an tsaron aikin gaggawa (RRS) na rundunar 'yan sandan jihar Legas sun hana wani mai talla, Rabiu Nafiu, kashe kan sa ta hanyar fadawa cikin ruwa a Legas.

A cikin wani jawabi a kafar su ta sadarwa, 'yan sandan na RRS sun bayyana cewa an hana mai tallar fadawa cikin ruwan ne da misalin karfe 8:00 na safe.

Kamar yadda suka bayyana, bayan Rabiu ya ga 'yan sandan na RRS na zuwa, sai ya gargadesu da kada su hana shi, sai dai 'yan sandan sun samu sun lallashe shi kafin ya yi tsalle daga saman gadar.

Jawabin ya kara da cewa mai tallar an tafi da shi cibiyar 'yan sandan ta RRS a karkashin umarnin shugabansu, CSP Olayinka Egbeyemi.

No comments

Powered by Blogger.