Header Ads

'Yan sanda a jihar Legas sun kama wani mutum dauke da yankakkun hannuwan mutum

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, CP Alabi Abiodun Sylvester

'Yan sanda a jihar Legas sun kama wani mutum mai shekaru 31, Monday Alfred, a yankin Imota da ke Shagamu a jihar Legas da zargin dauko hannuwan mutane biyu a cikin wani buhu.

Wata kungiyar sintiri ce daga Imota Division suka kama Alfred a ranar Laraba da misalin karfe 2:15 na yamma a kan titin Ori-Okuta Old Shagamu Road, kamar yadda kakakin 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana a cikin wani jawabi.

Kakakin ya bayyana cewa kungiyar sintirin sun tsayar da Alfred da kuma wani mutum daya da ke tare da shi ne a kan wani mashin mai namba JBG 276 VU yayin da suke sheka gudu daga Shagamu domin zuwa Imota. 

"Daya daga cikin wadanda ake zargin ya yi tsalle ya dira kasa daga kan mashin din tare da rugawa cikin daji a yayin da kungiyar sintirin ta tsayar da su.

"An yi tsere da su sosai wanda sakamakon haka ne aka kama Monday Alfred da ke zaune a Isale-Aye Araromi Imota, wanda shine ke tuka mashin din.

"A yayin da aka gudanar bincike sosai a cikin wani bakin buhu da suka dakko, sai aka ga yankakkun hannuwa biyu da ake zargin sasssan jikin mutum ne a cikin wani ruwa da ake zargin giya ce da ke cikin wani bokitin roba." Kamar yadda kakakin ya bayyana.

Hundeyin ya bayyana cewa bayan mashin din, an samu wata wayar Techno da kuma wata wayar Vivo daga wurin wadanda ake zargin.

Ya bayyana cewa ana kan kokari wajen kamo wanda ya gudu daga cikin wadanda ake zargin.

No comments

Powered by Blogger.