'Yan bindiga sun sace wani dan Turkiyya tare da wani mutum a Abuja
'Yan bindiga sun sace wani dan kasar Turkiyya, Erdogan Guler, dan shekaru 52 tare da kuma wani mutum wanda ba a iya tantance ko waye ba a Kubwa da ke Abuja.
Saturday PUNCH ta ruwaito cewa al'amarin ya faru ne da misalin karfe 7 na dare a ranar Laraba, 3 ga watan Mayun shekarar 2023, kuma an sanar da faruwar lamarin ga Byazin "Police Division " da ke Abuja.
Wata kwakkwarar majiyar 'yan sanda wadda ta tabbatar da al'amarin ga Saturday PUNCH ta bayyana cewa, "Wani mai hada kayayyakin da suka shafi katako, Babagana Usman, ya kawo rahoto kamar karfe 7 na dare a ranar Laraba, 3 ga watan Mayu, cewa wasu 'yan bindiga guda uku da ba a san ko su waye ba a cikin motar Toyota Prado SUV, wadda kuma kawo yanzu ba a san nambar ta ba, sun sace wani dan kasar waje, Erdogan Guler, dan shekaru 52, da kuma wani mutum daya wanda sunansa da adireshin sa kawo yanzu ba a sani ba da ke harabar inda Guler ya ke na Learner Estate da ke Brickcity a Kubwa."
Majiyar ta bayyana cewa wadanda suka sace su din tana iya yiwuwa suna aiki ne da wani wanda ke fada masu wurin da Guler ya ke.
"Sai dai jami'an da ke fada da yin garkuwa da mutane na SCID na yin bincike cikin al'amarin kuma 'yan sanda na iya kokarinsu wajen ganin sun ceto wadanda aka sace din tare da kama batagarin." Majiyar ta bayyana.
A yayin da aka tambaye ta a kan al'amarin, jami'a mai kula da hulda da jama'a ta rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa ba ta a cikin kasar.
"Kuma ba a sanar da ni al'amarin ba, amma zan bincika in dawo gareku." Kamar yadda Adeh ta bayyana.
Post a Comment