Header Ads

'Yan bijilanti sun ceto wata yarinya sabuwar haihuwa da aka gani a bola a jihar Ribas

Yarinyar da aka tsinta

'Yan bijilanti sun ceto wata yarinya da aka wurgar a bola a gaban wani wuri da ake kira Mile 3 Park, Diobu da ke Fatakwal babban birnin jihar Ribas a cikin daren ranar Juma'a.

Shugaban 'yan bijilanti a yankin Nkpolu Orowonrukwo, Mile 3 Diobu, Kwamaret Godstime Ihunwo ya bayyanawa PN NEWS cewa yarinyar an same ta ne lullube a cikin zani a cikin wani katan da aka wurgar a bola da misalin karfe 3:00 na dare yayin da suke yin sintiri.

Ya kara da cewa an samu yarinyar da cibiyar ta a jikin ta ba a cire ba a yayin da ta ke kokarin ganin ta rayu.

"Da misalin karfe 3:00 na daren ranar Juma'a, 28 ga watan Afirilun shekarar 2023 yayin da muke sintiri, na tsinci yarinya sabuwar haihuwa wadda ba ta kai awanni shida da haihuwa ba. A lokacin da aka tsinci yarinyar, tana lullube da zani da cibiyarta ba a yanke ba. 

"Na ceto yarinyar tare da kiran wata mata nas domin samun kulawar lafiya ga jaririyar cikin gaggawa. Bayan an bincika ne aka gane cewa yarinya ce mace jinjira." Kamar yadda shugaban 'yan bijilanti din ya bayyana.

Kwamaret Ihunwuro ya bayyana cewa yana tare ne da lauya mai kare hakkin bil-adama, Prince Wiro, domin zuwa a hukumance su sanar da 'yan sanda al'amarin a ofishin 'yan sanda na Nkpolu.

Ya ma yi roko ga gwamnatin jihar Ribas da ta yi magana da 'yan kwangilar da ke kula da fitilun kan titi a titin Ikwerre da su tabbatar da cewa akwai haske a tsawon dare domin gujewa afkuwar al'amari irin wannan. 

Rundunar 'yan sandan jihar ta Ribas ta tabbatar da ceto sabuwar haihuwar da aka yi ta bakin kakakinta, SP Grace Iringe-Koko a cikin wani jawabi da ta gabatar da misalin karfe 4:20 na safiyar ranar Juma'a, 28 ga watan Afirilun shekarar 2023, kuma a cikin jawabin ta bayyana cewa a yayin da ake cigaba da bincike, an tafi da yarinyar gidan kananan yara wadanda basu da iyaye mata na Borokiti da ke Fatakwal.

No comments

Powered by Blogger.