Yadda Dangote ya yi tasiri kan dabi'una a ɓangaren kuɗi - David Adeleke (Davido)
Mawaki dan Nijeriya, David "Davido" Adeleke, ya bayyana cewa wanda ya fi kowa arzuki a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya yi tasiri dangane da dabi'unsa a bangaren kudi.
Mawakin dan Nijeriya ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawar Forbes lokacin da ya ke a kasar Botswana domin taron Forbes 30 Under 30.
Randall Lane, wanda ya ke shine Cheif Content Officer na Forbes din (CCO), shi ya yiwa Davido tambaya, wanda an san shi da son motoci masu tsada da rayuwa ta facaka da dukiya, dangane da menene alakarsa da Dangote.
Davido ya tabbatar da cewa mahaifinsa, Chief Adedeji Adeleke, wanda biloniya ne abokin Dangote ne. Ya ma bayyana cewa a kodayaushe Dangote na ba shi shawarar ya rinka ajiye kudadensa ko kuma ya jujjuyasu.
"Kawu Dangote biloniya ne na daban. Kawu Dangote ya kan sayi sabuwar mota ne kamar sau biyu a cikin shekaru takwas. Shi mutum ne mai horo sosai kuma shi biloniya ne na daban.
" A duk lokacin da na gan sa, zai ce, "Ka ajiye kudin ka." Ba wani abu kuma da ya ke fada min na daban, kodayaushe ka ajiye kudin ka. Shi da mahaifina abokai ne sosai.
"Kuma shi (Dangote) ya yi abin alkhairi a gare mu ('yan Nijeriya) a gida. Ya bude masana'antu masu yawa. Ba da dadewa ba ya bude masana'anta mafi girma a Afirka. Wannan na samar da ayyukan yi." Kamar yadda mawakin ya bayyana.
Dangote, wanda aka kiyasta dukiyarsa da cewa ta kai dalar Amurka biliyan 20.5, shine ya fi kowanne mutum arzuki a Afirka, bakar fata wanda ya fi kowanne bakar fata arzuki a duniya kuma na 83 a duniya a jerin wadanda suka fi kowa arzuki a duniya kamar yadda Bloomberg Billionaires Index ya nuna.
Post a Comment