Wata motar bas da ta kwaso daliban Nijeriya daga Sudan ta kama da wuta
Wata motar bas da ta kwaso daluban Nijeriya da suka makale a babban birnin kasar Sudan, Khartoum, ta kama da wuta da safiyar ranar Litinin.
A matsayin rukuni na biyu na kwashe su din da gwamnatin tarayya ke yi, wannan motar bas din ta kwaso daluban Nijeriya ne akalla su 50 kuma tana da alamar (Katsina 1) a jiki, inda kuma ta nufi Port Sudan yayin da ta lalace sakamakon zafi mai yawa daga daya daga cikin tayoyin motar.
Motar dai ta kwaso dalubai 50 ne (49 maza 1 mace), a cikinsu har da Dr. Hashim Ibrahim Na'Allah, shugaban kungiyar dattawan Nijeriya a Sudan.
Kafin tayar motar ta fashe kuma wutar ta kama, direban motar ya tsaya ne a wani shinge na dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF), inda daga bisani aka rarraba 40 cikin 50 na daluban cikin wasu motocin bas din da suka kwaso daluban.
Sani Aliyu, wanda ya ke a Sudan, ya bayyana cewa al'amarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na dare lokacin kasar Sudan, kuma duka daluban sun tsira ba tare da wani abu ya shafe su ba, inda ya bayyana cewa dakarun na RSF sun yi iya taimakonsu ga fasinjojin tare da ba su kofin shayi da safe kafin su tafi.
Daga bisani sun cigaba da tafiya. Sakamakon wahalar da aka fuskanta a yayin daukar 'yan Nijeriya da tsallakawa ta kan iyakar Misra, a yanzu sama da 'yan Nijeriya 1000 ne za a kwashe ta hanyar Port Sudan.
Post a Comment