Wata mata ta kashe dan ta tare da dafawa da cin wani ɓangaren kansa
Wata mata mai suna Hanaa mai shekaru 29 ta buge dan da ta haifa mai suna Youssef da adda har ya mutu a gidan su da ke Misra, daga bisani kuma ta tafasa tare da cinye wani bangaren kansa.
Hanaa ta kashe dan na ta ne da duka hudu a kai kafin daga bisani ta yanyanka jikinsa a dakin wanka.
'Yan sanda sun kama Hanaa ne bayan kawun Youssef, wanda ya razana, ya ga bangarorin jikin yaron a bokiti a cikin gidan iyalinsu da ke kauyen Abu Shalabi.
Kamar yadda DailyMail ta bayyana a ranar Talata, matar, wadda ta amince da cewa ba ta da cikakken hankali, ta bayyanawa 'yan sanda cewa ta cinye wani bangaren kan yaron ne "domin tana so ya kasance tare da ita," inda ta kara da cewa ta dafa kan yaron ne da wani bangaren namansa a murhun risho a cikin tafasasshen ruwa kafin ta ci.
Matar wadda ta bayyana cewa ba ta da niyyar kashe dan nata, tana zaune da dan ne su kadai tun bayan rabuwa da mijin ta, wanda ya yi ikirarin cewa tana sane da abinda ta ke yi.
Tsohon mijin na ta wanda aka bayyana farkon sunansa da H.A, ya bayyana cewa, "A lokacin da na zo, 'yan sanda sun hana ni ganin da na saboda kazancewar wurin da al'amarin ya faru.
"Na rabu da ita shekaru hudu da suka gabata saboda tana da wani wuri da mahaifinta ya ba ta, sai ta ce min in bar gidana in bi ta da iyalaina mu zauna tare da ita a can.
"Sai na ki yarda, auren kuma ya zo karshe sakamakon hakan ta zaba, na yi kokarin in sasanta da ita bayan sakin, amma sai ta ki yarda ta kafe kan ra'ayin ta.
"Da na shi ne abin da ya hada alakata da ita, na kan je in gan shi akai-akai, in sai masa kaya da wasu abubuwan da yake bukata.
"Amma a 'yan kwanakin nan tana ta kokarin rabani da shi tare da shuka kiyayyata a zuciyarsa, yadda ba zai zo wajena ba."
Kamar yadda lauyansa Samir Mohamed Saleh ya bayyana, wadda ake zargin hankalin ta kwance a lokacin da ta fadawa masu yi mata tambayoyi, "Ina so ne in tseratar da kai na da kuma shi.
"Ina so ne in dauki fansa a kan mahaifinsa in kuma tsira. Babansa na ta zuwa akai-akai kuma yana so ya dauke shi a kodayaushe.
Ofishin yanke hukunci kan laifuffuka na kasar Misra ya bayyana cewa ana tsare da wadda ake zargin kuma za a yi mata gwaje-gwajen kwakwalwa.
Post a Comment