Header Ads

Wata kotu a Iran ta ba Amurka umarnin biyan diyyar dalar Amurka sama da miliyan 300 sakamakon hare-haren ta'addancin shekarar 2017 a Tehran

Hotunan wasu da suka rasu sakamakon hare-haren ta'addancin na 7 ga watan Yunin shekarar 2017 a Tehran

Kotu a Tehran ta yanke hukuncin cewa dole Amurka ta biya miliyoyin daloli a matsayin diyya ga iyalan wadanda hare-haren ta'addanci har sau biyu ya shafa a Tehran cikin shekarar 2017.

Mataimakin shugaban sashen shari'a na Iran, Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hukuncin a ranar Laraba: kamar yadda ya ke a cikin hukuncin, gwamnatin kasar Amurka da mutane tara da kamfanoni wadanda suka hada da tsofaffin shugabannin Amurka, Barack Obama da George W. Bush, Janar din Amurka mai ritaya Tommy Franks, hukumar CIA, Central Command na Amurka, sashen baitul mali na Amurka, Lockheed Martin Corporation da kuma American Airlines sai sun biya dalar Amurka miliyan 9.95 domin diyyar da ta shafi kudi da kuma dalar Amurka miliyan 104 domin diyyar da ta shafi mutunci hade da dalar Amurka miliyan 199 domin diyyar yunkurin musgunawa, inda duka kudaden da aka ci su tara suka kama kusan dalar Amurka miliyan 313.

Kotun ta karanto wasu bangarori daga jawaban manyan jami'an kasar Amurka dangane da rawar da kasar ta taka wajen shiryawa da bayar da umarni ga kungiyoyin 'yan ta'adda, musamman rawar da hukumar leken asiri ta CIA ta taka wajen kirkiro kungiyoyin ta'addanci, ciki kuwa harda Daesh. 

A ranar 7 ga watan Yunin shekarar 2017 ne aka kaddamar hare-hare a majalisar kasar Iran da kuma kabarin Imam Khomeini a Tehran. 'Yan bingida hudu, wadanda suka yi shigen mata suka shiga majalisar ta Iran tare da bude wuta ga matsaran da ke wurin, a bangare guda kuma, wasu 'yan bindigan suka kai hari a kabarin Imam Khomeini, inda suka bude wuta ga mutanen da ke harabar. Akalla mutane 17 ne suka rasu a yayin da wasu kusan 50 suka jikkata a hare-haren wadanda daga baya kungiyar Daesh ta ce ita ke da alhakin kaiwa.

Hukuncin na ranar Laraba ya zo ne sakamakon koken da iyalan wasu mutane uku da suka rasu da kuma na wasu mutane shida da suka jikkata a hare-haren ne suka shigar. Kotuna da dama a Amurka a cikin 'yan shekarun nan sun sha yanke hukuncin cewa a biya diyya dangane da kadarorin Iran da aka kwace da wadanda abubuwa daban-daban suka shafa a duniya, ciki har da hare-haren 11 ga watan Satumba.

No comments

Powered by Blogger.