Header Ads

Wata budurwa na neman kafa tarihi, inda ta fara kirgi ko ƙwayar shinkafa nawa ne a cikin buhu ɗaya

Wata buduwa 'yar Nijeriya, a kokarin ta na kafa tarihi kamar yadda kafar watsa labaru ta Legit Hausa ta ruwaito, ta fara kirga shinkafar da ke cikin buhun shinkafa domin sanin ko shinkafa nawa ce a ciki.

A cikin wani bidiyo wanda wani mai suna @prize303 ya wallafa, an ga yadda budurwar a cikin natsuwa ta ke kirga shinkafar da ke cikin buhun da kuma lissafa yawan abinda ta samu.

Budurwar ta sha alwashin sai ta kirga shinkafar da ke cikin buhun dukanta ba tare da gajiyawa ba.

Wannan faifan bidiyo na budurwa mai son sanin ko shinkafa nawa ce a cikin buhu daya tuni ya haifar da martani daban-daban daga masu amfani da kafofin sada zumunta. 

Abinda ba a sani ba shine girman buhun shinkafar, amma dai kawo yanzu ta kirga kwayar shinkafa da ta kai 13,000.

A yayin da ta ke kirgar, tana rike takarda ne domin rubuta duk abinda ta kirga saboda kada ta manta. 

A cikin jama'ar da ke tofa albarkacin bakin su kan wannan al'amari, wasu daga ciki sun yiwa budurwar fatar nasara.

No comments

Powered by Blogger.