Header Ads

Wani yaro ya tseratar da 'yar uwarsa daga mai garkuwa da mutane ta hanyar amfani da gwafa.

Wani yaro dan kasar Amurka mai shekaru 13, Deedaye Marksman, ya tseratar da 'yar uwarsa daga yin garkuwa da ita ta hanyar yin amfani da gwafa.

Yarinyar mai shekaru takwas na neman wani abu ne da ake kira naman kaza ko lemar kwadi a satin da ya gabata a bayan gidan su da ke Alpena Township da ke Jihar Michigan a kasar Amurka, inda wani mutum da ba a san ko waye ba ya tsallako ta shingen gidansu ya kama ta, kamar yadda 'yan sanda a jihar da ke arewacin Amurka suka bayyana a cikin wani jawabi a ranar Litinin ga kafar watsa labaru ta AFP. 

Sai ta fara kokarin kubutar da kan ta. Sai dai a yayin da yarinyar ta kubuta lokacin ne shi kuma yayan na ta mai shekaru 13 ya dakile yunkurin sace ta din.

Yaron, wanda ya shaida yadda al'amarin ya faru, "ya harbi wanda ake zargin da gwafa a kai da kuma kirji." Kamar yadda wani dan sanda ya bayyana.

Wanda aka harba da gwafar sai ya gudu daga wurin da al'amarin ya afku, amma jami'an tsaro nan-da-nan suka zo yankin tare da ganowa da kama shi, dan shekaru 17 "tare da alamun jin rauni wanda ya yi daidai da wanda za a samu daga harbin gwafa" kamar yadda 'yan sanda suka bayyana.

Wanda ake zargin an caje shi da yunkurin yin garkuwa da wani da kuma yunkurin yaudarar yara kuma za a yi masa hukunci a matsayin babban mutum kamar yadda kafar watsa labaru ta AFP ta ruwaito.

No comments

Powered by Blogger.