Wani mutum ya kashe matar da ya saki bayan samun labarin za ta sake yin aure
Wani mutum mai suna Aminu Abubakar mai kimanin shekaru 56 a duniya ya kashe tsohuwar matarsa, Nana Fadimatu, mai kimanin shekaru 38 da haihuwa sakamakon dukan ta da ya yi kuma dukan ya zama sanadiyyar rasuwarta, biyo bayan samun labari da ya yi cewa za ta sake yin aure.
Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar Adamawa suka kama mutumin da ake zargi da kisan wanda ke zaune a Unguwar Lelewaji, Shagari Estate da ke karamar hukumar Yola ta Kudu.
An bayyana cewa Aminu ya je wajen tsohuwar matarsa Nana Fadimatu ne da misalin karfe 10 na dare a ranar Juma'ar da ta gabata bayan samun labarin za ta yi aure, yayin da suke ganawa sai fushi ya debe shi inda ya rika bugunta da wani abu mai nauyi da ke hannun sa wanda nan ta ke ta suma, daga baya kuma ta rasu.
Bayan samun labarin, wanda zai aure ta mai suna Mahmud Rufai wanda ke zaune a Unguwar Shagari Annex, sai ya hanzarta ya kai maganar ga 'yan sanda da ke Shagari Police Division, inda su kuma suka kama wanda ake tuhumar tare da tafiya da shi ofishin su.
Allah Ya yi mata rahama Ya kuma raba mu da mummunar kaddara.
Post a Comment