Header Ads

Wani mutum da matarsa sun yi garkuwa da kansu tare da neman kudin fansa naira miliyan 5 a jihar Legas

Taswirar Nijeriya

An kama wani mutum da matarsa mazaunan jihar Legas sakamakon yin garkuwa da kansu da suka yi tare da neman kudin fansa naira miliyan 5 daga iyalansu.

Mutumin dan shekara 53 wanda ya ke mai fasahar ayyukan hannu, da matarsa 'yar shekara 48, an kama su ne ranar Laraba da kuma Alhamis bayan wani daga cikin iyalan nasu ya kai rahoton ikirarin yin garkuwar da su ofishin 'yan sanda inda kuma ma'auratan suka amsa laifinsu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa ma'auratan sun amsa laifinsu, inda suka bayyana cewa sun shirya su yi garkuwa da kansu ne domin su samu naira miliyan 3 domin sake sayen gidansu da ke Badagry a Legas.

"Mutumin shi ya yi shawarar yin hakan kuma ya fadawa matarsa. Bai karyata ba a gaban 'yan sanda. Ya ce ya yi hakan ne ta hanyar sakon waya (text message). Ya ce ya yi hakan ne domin ya sake sayen gidansa a kan kudi naira miliyan 3 a yankin Badagry.

"Mutumin ya ce ya shirya yin garkuwa da kansu ne domin duk cikin 'yan uwansa maza da mata ba wani mai kudi sosai kuma wadanda ke kasashen waje a cikin 'yan uwan nasa suna a shirye domin su taimaka masa ta hanyar kudi.

"Ya yi ikirarin cewa in har suka ji cewa an yi garkuwa da shi da matarsa, za su daidaita da masu garkuwar kuma za su biya kudin." Kakakin ya bayyana kamar yadda mutumin ya yi bayani.

Hundeyin ya bayyana cewa ma'auratan suna zaune a gidansu lokacin da suka turawa 'yan uwan nasu sakon yin garkuwar da su ta waya, kuma a lokacin da 'yan sanda suka je gidan a ranar Talata sai suka samu matar da 'ya 'yansu uku.

Ya bayyana cewa 'yan sandan sun nemi matar da ta zo su tafi ofishin su amma sai ta roke su da su bari ta zo ranar Laraba, inda suka amince mata kuma ta zo a ranar Laraba din aka kuma kama ta da tuhumar yin garkuwa da kai yayin da shi kuma mijin aka kama shi a ranar Alhamis.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa ma'auratan sun yi nadamar laifin da suka aikata tare da neman gafarar iyalansu da kuma na 'yan sanda, inda suka ba jama'a shawarar kada su ji suna shawa'ar aikata laifi ko kwadayin arzukin iyalansu ko na wasu jama'an.

Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba za a gurfanar da ma'auratan a kotu.

No comments

Powered by Blogger.