Header Ads

Wani hari da jirgin yaƙin Isra'ila ya kashe wani ƙaramin yaro a Gaza

Tamim Daoud

Wani yaro bafalasdine ya rasu sakamakon firgici bayan wani hari da jirgin yakin Isra'ila ya kai a yankin al-Remal da ke tsakiyar zirin Gaza.

Kamar yadda majiyoyin yankin suka bayyana, yaron dan shekaru hudu mai suna Tamim Daoud ya kwanta a daren Litinin cike da burin yin bikin zagawowar ranar haihuwarsa na cika shekaru biyar a wata mai zuwa.

Sai dai ya farka shi da sauran 'yan uwansa da karfe 2:00 na dare sakamakon karar hare-haren Isra'ila.

"Yarona Tamim na barci yayin da harin Isra'ila ya samu wani gidan da ke dauke da mutane da ke kusa da gidan mu." Mahaifin yaron mai suna Mohammed ya bayyana. "Ya farka cikin jin tsoro a razane."

Karar harin na da karfi sosai. Winduna sun farfashe kuma yankin ya tarwatse.

Tamim ya yi kuka sosai yayin da mahaifiyarsa ke kokorin kwantar masa da hankali domin ya koma barci. Kamar yadda mahaifinsa ya bayyana, sai yaron ya kasa numfashi, inda ya fara yin iya kokarinsa wajen ganin ya yi numfashi.

Daga karshe dai Tamim ya koma barci. To amma bayan awowi biyar sai ya cigaba da kokarin kuma. Ya kara samun wani firgicin.

"Na hanzarta domin kai shi asibiti." Mahaifinsa ya bayyana, "Amma zuciyarsa sai ta daina aiki a yayin da muke kan hanya." 

A asibiti Tamim ya samu kulawa, amma zuciyarsa kadan ta ke bugawa. "An shigar da yaron nawa sashen kulawa ta musamman inda kuma likitocin suka bayyana min cewa ya rasu kafin gari ya waye." Kamar yadda Mohammed ya bayyana.

"Zuciyar yaro na ba za ta iya jurewa tashin hankalin hare-hare ba." Mahaifin ya bayyana.

A ranar Alhamis, babbar sakatariyar kungiyar kasashen musulmai (OIC) da kakkausar murya ta yi Allah wadai da "munanan hare-haren soja" da ake kaiwa a zirin Gaza, inda ta bayyana su da "babban laifi ne kuma keta dokokin kasa-da-kasa ne da kuma ka'idoji jin kai."

No comments

Powered by Blogger.