Header Ads

Wani dan sanda ya rasu, mutane hudu sun jikkata sakamakon harin bam a wata mota wanda kungiyar IS ta kai a Damascus


Wani dan sandan Siriya ya rasu yayin da wasu mutane hudu suka jikkata sakamakon harin bam da kungiyar IS ta kai a wata mota a wani ofishin 'yan sanda na kasar Siriya. 

Ma'aikatar cikin gida ta kasar Siriya ta bayyana cewa motar ta tarwatse ne a ofishin 'yan sanda na Barzeh da ke arewacin babban birnin kasar, inda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar wani Laftanar Kanar da kuma jikkatar wasu mutane hudu.

"Bincike na cigaba da gudana a yanzu haka domin gano yadda al'amarin ya faru." Ta kara da bayyanawa a cikin bayanin tare da nuna hotunan motar wadda ta kone.

Daga baya kungiyar IS ta bayyana cewa ita ke da alhakin kai harin, inda ta bayyana cewa mambobinta "sun sanya tare da tada abun fashewa a cikin wata mota da ke ofishin 'yan sanda" kamar yadda suka bayyana a Telegram din su.

Wannan dai hari ne nasu da ba kasafai ake ganinsa a Damascus ba wadda ta samu sauki daga fadace-fadace a cikin shekarun na, musamman tun bayan da gwamnati ta karbi iko da wurin da ya ke hannun 'yan tawaye na karshe a kusa da babban birnin a cikin shekarar 2018.

Sai dai abubuwa da suka shafi tsaro, ciki harda fashewar abubuwa da niyyar kaiwa sojoji hari ko motocin fararen hula, na cigaba da faruwa a Damascus.

A cikin watan Oktobar 2022, harin bam a kan motar sojojin kasa na Siriya a kusa da Damascus ya yi sanadiyyar rasuwar sojoji 24.

Kungiyar kare hakkin bil-adama ta "The Syrian Observatory for Human Rights" wadda kungiya ce da ke Birtaniya mai sa ido a kan yaki, ta dangantaka harin da kungiyar IS.

A watan da ya gabata, kafofin watsa labarai mallakar kasa sun bayyana cewa wani harin bam wanda ba a samu wanda ya dauki nauyin yin sa ba ya afku a wani yanki, inda ma'aikatar cikin gida ta bayyana cewa mutane biyu sun samu raunuka kadan.

Wuraren da kungiyar IS ta shimfida "kalifanci" wanda ya kwashi fadin kasa mai girma a cikin kasar Siriya da Iraki ya zo karshe ne a gabashin Siriya a farkon shekarar 2019.

Yakin na Siriya ya yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 500,000, miliyoyin sun rasa muhallansu yayin da kuma ya lalata masa'antu da kayayyakin amfanin jama'a a kasar.

Wani bangare mai fadin gaske a arewacin kasar ta Siriya har yanzu ba karkashin ikon gwamnati ya ke ba.

No comments

Powered by Blogger.