Header Ads

Ukraine ta nemi Jamus da ta samar mata mizayel masu cin dogon zango waɗanda za su iya kai wa Moscow

Kasar Jamus ta bayyana cewa ta samu roko a hukumance daga Ukraine da ta samar ma ta da mizayel din Taurus wanda ake harbawa daga sama-zuwa-kasa, wanda zai iya ba Kiev damar samun wurare cikin kasar Rasha domin nisan su na kilomita 500.

Ma'aikatar tsaron Jamus a ranar Asabar ta bayyana cewa, "Ta samu wani roko daga bangaren Ukraine a cikin 'yan kwanankin nan."

Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya nemi a basu makaman mizayel din ne a yayin wata tafiya da ya yi Berlin a farkon watan Mayu, kamar yadda kafofin watsa labaru na kasar Jamus suka bayyana.

Masanin kimiyyar siyasa dan kasar Jamus, Mattia Nelles, ya ce Ukraine ta yi alkawarin ba za ta harbi wuraren da ke cikin Rasha ba. Sai dai ya ce wannan makamin mai cin dogon zango ya damu shugabancin kasar Jamus.

"Akwai tambayoyi da ba a warware ba wadanda suka shafi bayanan ina aka harba kuma abu mai muhimmanci tambayar da ta shafi siyasa ta ko gwamnatin Jamus na da niyyar samarwa Ukraine manyan makaman da za su iya harbo Moscow." Ya bayyana.

Kiev a hukumance ta yi amfani da makamin Storm Shadow wajen harbin wuraren da Rasha ke ajiye kayayyaki da kuma wuraren ta na bayar da umarni wadanda ke da nisa daga kan iyakar da ake yaki a wuraren da Rasha ce ke da iko da su a gabashin Ukraine tun cikin watan Mayu.

A farkon watan nan Rasha ta bayyana cewa Ukraine ta yi amfani da makamin miyazel din Birtaniya na Storm Shadow wajen harbo wuraren da suke na farar hula ne a yankin da ke karkashin ikon Rasha.

 Ta kuma cigaba da yin gargadi ga kasashen yamma akai-akai kan samar da makaman mizayel masu cin dogon zango, inda ta bayyana cewa hakan zai sa yakin ya ta'azzara.

Sai dai kasashen yamma sun cigaba da samarwa Ukraine din kayayyakin soji na biliyoyin daloli tun bayan fara yakin da Rasha ta yi a Ukraine a cikin watan Fabrairu da ya gabata.

No comments

Powered by Blogger.