Sojojin Sudan sun kai hare-hare ta jiragen sama a Khartoum, duk da cewa an tsaigaita wuta
Sojojin Sudan sun kai hare-hare ta jiragen sama a babban birnin kasar Sudan, Khartoum, kan sansanonin jami'an tsaron da ba sojoji ba duk da cewa sun amince da a kara wa'adin tsagaita wuta.
Sojojin sun bayyana cewa jiragen yakin su sun kai hari kan dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF)a Khartoum a ranar Alhamis.
Sojojin a yammacin ranar Laraba sun bayyana cewa sun amince da a tattauna a Juba, babban birnin makwafciyar kasar ta Sudan ta Kudu, a kan kara tsawaita wa'adin tsagaita wutar da aka yi na kwanaki uku wanda ya kawo karshe a ranar Juma'a karkashin jagorancin IGAD, wata kungiya ta kasashen gabashin Afirka.
An dai sha yin yarjejeniyar tsagaita wuta tun bayan barkewar fadan a tsakiyar watan Afirilu a tsakanin sojoji wadanda Janar Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta da kuma RSF, wadanda mataimakinsa wanda ya zama abokin gaba Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta.
Sai dai duka yarjejeniyoyin ba a yi nasara a cikinsu ba.
A yanzu dai mummunan fadan ya fadada daga babban birnin kasar zuwa yankunan kasar musamman yammacin Darfur, wanda dama ke fama da fadace-fadace.
Mutane kimanin 512 ne suka rasu a yayin da 4,193 suka raunata kamar yadda kididdigar ma'aikatar lafiya ta bayyana. Sai dai kididdigar yawan wadanda suka rasa rayukansu din ana zaton sun fi haka.
Post a Comment