Header Ads

Sojojin Sudan da dakarun RSF sun amince da a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimmawa


Bangarori biyu da ke fada da juna a Sudan sun amince da a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimmawa a wannan watan biyo bayan tashe-tsahen hankula akai-akai.

Bangarorin biyu daga farko sun amince da yarjejeniyar wadda aka cimmawa ta hanyar shigowar kasar Saudi Arabiya da Amurka a ranar 20 ga watan Mayu, inda kuma ta fara aiki awowi 48 bayan nan. Yarjejeniyar ta zo karshe a ranar Litinin da karfe 09:45 na dare agogon kasar (1945 GMT).

Sai dai duka bangarorin biyu sun yi ta keta ka'idojin yarjejeniyar, wanda hakan ya shafi aikin kawo kayayyakin agaji da daidaita al'amurra.

Kafin kawo karshen yarjejeniyar, kasashen da suka shiga tsakani a cikin wani jawabi sun bayyana cewa bangarorin biyu da ke fada da juna sun amince su kara tsawaita yarjejeniyar na tsawon kwanaki biyar, kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta ruwaito.

Jawabin ya bayyana cewa duk da cewa an keta ka'idojin yarjejeniyar, amma dai an iya samu an shigo da kayan agaji ga mutane kusan miliyan biyu.

"Tsawaita yarjejeniyar zai bayar da lokaci wajen cigaba da samar da kayan agaji, daidaituwar al'amurra da kuma tattaunawar yiwuwar kara tsawaita lokacin." Kamar yadda jawabin na wadanda suka shiga tsakani ya bayyana.

Wadanda suka shiga tsakanin sun bayyana cewa sojojin da dakarun RSF din "na nuna alamun cigaba da rikicin."

Reuters ita ma ta ruwaito wasu majiyoyi wadanda ke da ilimin yarjejeniyar na bayyana cewa tattaunawa domin yin gyararraki domin tattabar da yarjejeniyar na cigaba.

Hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya (WFP) ta bayyana cewa daga ranar Lahadi ta iya samu ta rarraba abinci a karon farko a babban birnin kasar Khartoum tun bayan fara yakin.

Yakin dai da ake yi a kasar da ke arewacin Afirka na yin nuni ne da yunkurin neman iko a tsakanin shugaban sojoji, Abdel Fattah al-Burhan, da mataimakinsa, Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da Hamedt, shugaban dakarun kai dauki domin tallafawa ayyukan tsaro (RSF).

Yakin na kasar Sudan ya yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 700 tare da raba wasu kusan miliyan 1.4 da muhallansu. Ana tsoron kididdigar gaskiya ta wadanda suka raunata da wadanda suka bar muhallansu ta fi haka, domin rashin iya shiga wuraren da ake yakin. 

Kafin tsawaita yarjejeniyar ta fara aiki ne a farkon ranar Litinin, an ruwaito cewa an yi arangama mai karfi a Khartoum da sauran birane.

A cikin satuttukan da suka gabata, ma'aikatu, ofisoshi, gidaje da bankuna duk an kwashe kayayyakin da ke cikinsu ko an lalata su a Khartoum. Wutar lantarki, ruwa da sadarwa mafi yawanci ba a cika samun su ba, kuma akwai karancin magunguna da kayayyakin kula da lafiya.

No comments

Powered by Blogger.