Header Ads

Shugaban sojojin Isra'ila ya bayyana damuwarsa kan yawan kashe kansu da sojojin su ke yi

Wasu sojojin Isra'ila 

Shugaban jami'an sojojin Isra'ila ya bayyana damuwa sakamakon yawan kashe kai a tsakanin rundunar sojojin Isra'ila tare da bukatar kara kaimi daga bangaren hukumomi.

Kamar yadda wani rahoto na kafar watsa labarun Isra'ila KAN ya nuna, Laftanar Janar Herzi Halevi, ya bayyana karuwar kashe kai a tsakanin rundunar sojojin Isra'ila da abu mai "hatsari kuma mai sa rashin kwarin gwiwa" ga sojojin kasar.

Shugaban sojojin ya bayar da umarni ga hukumar sojojin da su fito da wani tsari domin rage faruwar al'amarin.

KAN ta ruwaito cewa Isra'ila ta fuskanci hauhawar kashe kai a tsakanin sojojin kasar ta a shekarar da ta gabata, saboda wannan dalilin shugaban sojojin ya bayar da umarnin a kara yawan kayayyakin da ake bukata tare da samar da karin jami'ai domin kawo karshen al'amarin.

Kafar watsa labarun Isra'ila ta ruwaito cewa sojojin Isra'ila sun kashe kansu a farkon wannan watan da muke ciki, inda biyu daga cikin su sun kashe kansu din ne a cikin satin da ya gabata.

Kamar yadda kafar watsa labarun Palestine Today ta bayyana, kashe kai shine abinda ya fi haifar da mutuwa a tsakanin sojojin Isra'ila a lokutan da ba na yaki ba, kuma yawan masu kashe kansu din na kara hauhawa a cikin 'yan shekarun nan.

Kididdiga a hukumance daga cibiyar bincike da bayanai ta Knesset (majalisar Isra'ila) ya nuna cewa gwamnatin ta Tel Aviv na samun yawan wadanda suka kashe kansu 500 a duk shekara, 100 daga cikin su mutane ne matasa 'yan tsakanin shekaru 15 zuwa 24.

Sojojin Isra'ila sun samu hauhawar sojojin da aka kashe a cikin kaki - 44 ba kamar 31 ba a shekarun baya - tare da karin yawan wadanda ke kashe kansu kamar yadda kididdigar sojojin ta nuna a wannan shekarar.

Kashe kai na kasancewa abinda ya fi haifar da mutuwa, inda akalla sojoji 14 aka yi imanin cewa sun kashe kansu a shekarar 2022, ba kamar 11 ba a shekarar da ta gabata.

Mafi yawan sojojin da suka kashe kansu a shekarar da ta gabata sojoji ne da aka sanya su aikin na soja a dole cewar Birgediya Janar Yoram Knafo, wanda shine shugaban sashen kula da jami'ai, ga manema labaru, inda ya ce biyu a cikin sojojin 14 sojoji ne da ke cikin halin kadaitaka, sojojin da ko dai iyalansu ba su a yankunan da aka mamaye ko kuma iyalansu ba su taimaka masu a nan.

Sojojin na Isra'ila har wa yau sun ga hauhawar yawan sojojin da suka jikkata a shekarar 2022, mutum 158, ba kamar 92 ba a shekarar 2021.

No comments

Powered by Blogger.