Header Ads

Shaguna 100 sun kone sakamakon gobara a kasuwar 'Yan - Katako, Sabon Gari Zariya a jihar Kaduna

Kayayyaki na miliyoyin nairori sun kone a shaguna 100 da ke sananniyar Kasuwar 'Yan - Katako da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna a ranar Laraba.

Shugaban kasuwar ta 'Yan - Katako, Ahaji Mohammed Ashiru, ya shaidawa manema labaru a Zariya cewa gobarar ta afku ne a farkon awannin ranar Laraba.

Ashiru ya bayyana cewa masu tsaron kasuwar sun shaida masu cewa gobarar ta faru ne sakamakon wuta da ke kawowa daga wasu wayoyin da suka ratsa ta cikin kasuwar.

"Wutar da ke kawowa daga wayoyin sai ta dira kan silin da ke kasuwar, nan-da-nan kuma sai gobarar ta tashi." Kamar yadda ya bayyana.

Shugaban kasuwar ya bayyana cewa masu tsaron kasuwar sun kasa kashe wutar, inda ya ce sai da aka samu taimakon hukumar kashe gobara ta kasa sannan aka iya kashe gobarar bayan awanni.

Shugaban kasuwar ya jajantawa wadanda ibtila'in ya shafi shagunansu, inda ya neme su da su dauki al'amarin a matsayin kaddara.

DSF Abubakar Ibrahim, wani babban jami'i a ofishin kashe gobara, ya bayyana cewa rashin isasshen ajiyayyen ruwa ya haifar da jinkiri yayin yaki da gobarar.

Sai jami'in ya yi kira ga gwamnati da sauran mutane masu yunkurin kawo cigaba ga al'umma da su taimakawa hukumar da wuraren ajiye ruwa domin inganta ayyukansu.

No comments

Powered by Blogger.