Header Ads

Saudi Arabiya ta yanke wa wasu matasa 'yan Shi'a uku da ke Qatif hukuncin kisa

'Yan kasar Saudiyya, Haider bin Hassan Muwais, Hassan bin Issa Al Muhanna da Muhammad bin Ibrahim Muwais da aka yankewa hukuncin kisa a yankin da ya fi yawan 'yan Shi'a na yankin gabashi da ke Saudi Arabiya a ranar 22 ga watan Mayun shekarar 2023.

Hukumomin Saudi Arabiya sun yankewa wasu matasa uku da suka fito daga yankin da ke da yawan 'yan Shi'a na Qatif hukuncin kisa sakamakon caje-cajen shiga cikin ayyukan zagon kasa wadanda masu suka kan al'amarin suka bayyana da wani banagare ne na kokarin murkushe muryoyin da ke adawar siyasa.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya a cikin wani jawabi a ranar Litinin ta yi ikirarin cewa an tabbatar da hukuncin kisan ne ga Hassan bin Issa Al Muhanna, Haider bin Hassan Muwais da Muhammad bin Ibrahim Muwais.

Ma'aikatar ta yi ikirarin cewa 'yan kasar ta Saudiyya "Sun hadu da wata kungiya da ke kasar waje ne domin yin ayyukan ta'addanci a masarautar. An same su da laifin mallakar makamai da makaman harbi, fitar da mutanen da ake yiwa caje-cajen da suka shafi tsaro wajen kasar, shigowa da ajiye makamai domin hargitsa tsaron cikin gida." 

A baya a ranar 9 ga watan Mayu, hukumomin Saudiyya sun yankewa Anwar bin Jaafar bin Mahdi al-Alawi, wani dan kasar Saudiyya da ya fito daga yankin gabashi, hukuncin kisa a kan cajin "kai hari a ofishin 'yan sanda, taimako da kuma samar da mafaka ga mutumin da ake yiwa caje-cajen da suka shafi tsaro da kuma mallakar makamai."

Kotun laifuffuka ce ta samu Alawi da laifi kuma aka bayar da umarni na sarauta domin zartar da hukuncin kisan.

Yankin da ke da arzukin man fetur na Saudiyya kuma yankin gabashi wanda ya ke mafiyawan mutanensa 'yan Shi'a ne ya kasance wani wuri da ake ta gudanar da zanga-zanga tun cikin watan Fabrairun shekatar 2011. Masu zanga-zangar na bukatar a yi canje-canje ne, a samar da hakkin fadar albarkacin baki, a sako fursunonin siyasa da kuma kawo karshen rashin mutuntawa ta tattalin arzuki da addini da ake nunawa yankin.

Akan afkawa zanga-zangar da ake yi da karfi, inda kuma ake kara matakan tsaro a yankin baki daya.

Tun dai zamowar Mohammed bin Salman yarima a Saudiyya a shekarar 2017, hauhawar kama masu fafutika, masu rubuta abubuwa a kafafen sada zumunta, masana da wadanda ake gani a matsayin masu adawa ta siyasa ya karu, inda kusan ba a iya kawar da kai daga adawa ko yaya take duk da Allah wadai da ake yi daga kasashen duniya kan amfani da karfin. 

A sakamakon haka, an zartar da hukuncin kisa kan malaman addinin Musulunci kuma masu fafutikar hakkin mata an kulle su tare da azabtar da su yayin da 'yancin fadar albarkacin baki, yin kungiya da kuma abinda mutum ya yi imani da shi ake cigaba da hana su.

No comments

Powered by Blogger.