Header Ads

Saudi Arabiya na neman sasantawa da kungiyar Hezbollah bayan ta gyara alakarta da kasar Iran - Rahoto

Yariman Saudiyya, Muhammad bin Salman da babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyed Hassan Nasrallah

Rahotanni na bayyana cewa Saudi Arabiya na neman sasantawa da kungiyar fafutika da ke kasar Lebanon ta Hezbollah a yunkurin ta na baya-bayan nan na daidaita dangantaka a tsakanin ta da Siriya da kuma Iran.

Jaridar kasar Lebanon ta al-Akbar daily newspaper ta yi rahoton a ranar Asabar, inda ta kawo jawabin wani jami'in kasar Saudiyya wanda ba ta bayyana sunansa ba wanda ya yi ikirarin cewa masarautar na fatar fara sasantawa da Hezbollah "nan ba da jimawa ba."

Ta ma kawo wasu jawabai daga "majiyoyin da ba na musamman ba a Beirut" inda ta bayyana cewa sasantawar za a yi ta ne ta hanyar "wani wanda zai shiga cikin al'amarin na uku."

"Ko hakan ya yi nasara ko bai yi nasara ba, yana yin nuni da yadda Riyadh ke daidaita alakarta ne a yankin...," jaridar ta rubuta, inda ta bayyana canje-canje a tsarin siyasar masarautar "da wani abu da bai taba faruwa ba a baya."

Masu sharhi a kan al'amurra sun bayyana cewa a wannan canje-canje kan siyasar kasashen waje na Saudiyya tuni dai aka ga gyara dangantaka da Iran tare da nuna yunkurin gyara alaka da Siriya da kuma kungiyar fafutika ta Falasdinawa Hamas.

Saudi Arabiya ma na kara nesanta kan ta daga Amurka ta fannin tattalin arzuki da kuma a siyasance.

A cikin watan Maci, a watan da Riyadh da Tehran suka amince su daidaita dangantaka a tsakaninsu karkashin jagorancin kasar Sin, babban sakataren kungiyar Hezbollah, Sayyed Hassan Nasrallah, ya bayyana gyara dangantakar "da cigaba mai kyau."

Wadannan canje-canje a siyasar kasashen waje na kara samar da nakasu ga duk wani yunkurin "daidaita alaka" a tsakanin Saudi Arabiya da Isra'ila.

A yayin da ta ke magana dangane da wadannan canje-canje a ranar Litinin, jaridar kasar Isra'ila ta Maariv ta bayyana cewa, "Ana kyautata zaton cewa jirgin kasan Saudiyya ba inda zai tsaya sai tashar da ke dauke da katuwar alamar da aka rubuta Hezbollah a jiki." 

Wasu kafafen watsa labarun na Isra'ila suma sun bayyana cewa cigaba da gyara alaka da Saudiyya ke yi da kasashen da ba su shiri da Isra'ila abin tashin hankali ne ga Tel Aviv.

No comments

Powered by Blogger.